Ɗan wasan gaba na Jamus, Thomas Muller ya yi tsokaci game da ritayar sa daga buga ƙwallon ƙafa da ƙasar sakamakon fitar da su a gasar Euro 2024.
Jamus ta sha kashi a hannun Spain da ci 2-1 a wasan daf da na kusa da ƙarshe a Stuttgart ranar Juma’a.
- Chelsea Za Ta Fafata Da Real Madrid Da Manchester City A Amurka
- Makarantar Horas Da ‘Yan Kwallo Ta Katsina Zata Wakilci Nijeriya A Gasar Kofin Dana Na Denmark
Bayan kammala wasan, Muller ya yi tsokaci akan ko zai cigaba da bugawa ƙasar Jamus kwallo kokuma zai dakata haka ya gaya wa Sky Sport.
Watakila wannan shine wasa na na ƙarshe da tawagar ƙasar Jamus inji Muller a wata hira da yayi da kafar watsa labarai ta Sky Sport.
Muller ya fara bugawa Jamus wasa a shekara ta 2010, inda ya buga wasanni 131, ya jefa ƙwallaye 45, a shekarar 2014 ya taimakawa ƙasar Jamus lashe kofin Duniya a ƙasar Brazil.