Shugabannin kungiyoyin kwadago na ganawa da Shugaba Bola Tinubu don tattauna sabon mafi karancin albashin ma’aikatan Nijeriya.
Joe Ajaero daga NLC da Festus Osifo daga TUC, sun isa Fadar Gwamnati a Abuja don ganawar.
- Badakalar Kudade Fiye Da Miliyan 37: Kotu A Kebbi Ta Umarce CSP Rano Ya Nemo Shaidun Kare Kansa
- Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli Ta Ba Ƙananan Hukumomi ‘Yancin Cin Gashin Kansu
Gwamnati ta bayar da shawarar biyan Naira 62,000 a matsayin mafi karancin albashi, yayin da kungiyoyin kwadago ke so a biya Naira 250,000.
Wannan ganawar ta biyo bayan jawabin Shugaba Tinubu na ranar 12 ga watan Yuni, inda ya ce zai aike sabon tsarin mafi karancin albashin Majalisar Dokoki a matsayin kudiri.
A ranar 25 ga watan Yuni, Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta dage tattaunawa kan sabon albashin don bayar da damar yin shawarwari da masu ruwa da tsaki.
A ranar 27 ga watan Yuni, Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaba Kassim Shettima, sun gana da gwamnonin jihohi da ministoci don tattauna sabon mafi karancin albashin a taron Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa.