Ganawar da aka yi tsakanin shugaban kasa Bola Tinubu da shugabannin kungiyar kwadagon a ranar Alhamis ta kare ba tare da an cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata ba.
Bayan zama na tsawon sa’o’i, Shugaban Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC), Kwamared Joe Ajaero, ya shaida wa manema labarai cewa ba su tattauna batun kudi ba.
- Tinubu, Shettima Da Gwamnonin Na Ganawar Sirri
- Kotu Ta Tura Tsohon Ministan Wutar Lantarki Zuwa Gidan Yari
Bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar shirya wani taro a mako mai zuwa.
Sai dai kuma yayin da aka kara tambayarsa ko taron ya kai ga cimma matsaya kan bukatarsu ta neman a biya su mafi karancin albashi na Naira 250,000, Ajaero ya bayyana cewa za a tattauna batun ne a ganawar da za su yi da Shugaba Tinubu a nan gaba.
A nasa bangaren, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya (TUC), Kwamared Festus Osifo, wanda shi ma ya zanta da manema labarai, ya bayyana cewa shugabannin kungiyar kwadagon sun gana da shugaban kasar ne domin nuna damuwarsu kan halin kuncin da ‘yan Nijeriya ke ciki.
Sai dai Karamin Ministan Kwadago da Aiki, Hon. Nkeiruka Onyejeocha, wanda ya jagoranci taron, ya bayyana cewa, abubuwan da aka tattauna sun kasance masu amfani ga bangarorin biyu.