Fatima Ibrahim Abba Gana, tsohuwar ma’aikaciyar banki ce kana har ila yau marubuciya. A hirarta da BUSHIRA A. NAKURA, ta bayyana abubuwa da dama da masu karatu za su ji dadin karantawa game da rayuwarta na karatu da kuma ayyukan da ta yi har ma da wadanda take yi a halin yanzu.
Masu karatu za su so sunan sunanki da Tarihin ki a takaice.
Assalamu alaikum warahamatullah wabarakatuhu.
Ni dai sunana Fatima Ibrahim Abba Gana, an haife ni a garin Kaduna, ba ni da wani suna da ake yi mani lakabi da shi. Na girma ne a garin Kaduna, Sokoto da Minna. Ni ‘yar asalin jihar Barno ce amma girman Kaduna da sauran garuruwan Arewa, ban taba zaman Maiduguri ba amma muna yawan zuwa akai akai iyayena ma ‘yan Maiduguri ne gaba da baya kuma Kanuri ne. Na yi Nursery a makarantar Mawo Nursery School Minna.
Na yi makarantar Firamare a Command Children school Sokoto, daga nan na yi makarantar Sakandire a Labayi International schools Kaduna. Jami’a ce na je Jami’ar Ahmadu Bello Zariya na kuma Karanta Bsc Accounting. Na yi bautar kasa a gidan gwamnati na Jihar Osun a Osogbo. Na yi ‘Professional edams ta ACCA, 2000 (ITPAN) Independent Telebision Producers Association of Nigeria)’ na fito da kwalin kwarewa a (Producing, Scriptwriting and Directing).
Na yi makarantar GOETHE Institute Lagos na fito da digiri, ina magana da harshen Jamus, daga nan na shiga banki na yi aiki na shekaru sha biyar har sai da na kai ga mukamin manaja ta wani sashen Banki, sannan na bude kamfanin Shawullam Nigeria Limited. Na zama MD / CEO na shiga harkar rubuce-rubuce ina kuma rubutu da Turanci da Hausa, ina da littafi Rakiba da Hausa da Turanci mai shafi 447 na soyayya, Karima a Hausa mai shafi 87 amma ni ba Bahaushiya ba ce, ni Kanuri ce kuma yanzu haka ina cikin manyan kungiyoyin marubuta kamar na gida Nijeriya da duniya kamar haka; SYNW (kungiyar marubuta matasa ta Mijeriya),IWWG ( kungiyar marubuta mata ta kasa da kasa, sai kuma kungiyar marubuta ta kasa da kasa ( IWA) domin yanzu haka ni ce ma P (Shugabar) wannan kungiyar reshen Nijeriya.
Me ya ja hankalinki a aikin banki?
Kin san wani lokacin sha’awa ce wasu kuma iyaye ne ke zaba masu. Ni na zabi aikin banki ne don sha’awa kuma ina son lissafi tun ina karama iyayena ba su zaba mani ba, don sai da na samu aikin don ni na nema da kaina sannan na kawo masu shaidar samun aikin. Na kuma samu damar yin aikin da banki, amma na fi son aikin fiye da komai shi ya sa na yi har shekaru goma sha biyar sannan na yi ritaya.
Me ya sa kika bar aiki?
Haka kawai na bar aiki don kashin kaina da mutunci da daraja a matsayin manaja ba tare da an kore ni ba.
Kina da aure ko kin taba yin aure?
Ban taba aure ba.
A yanzu a wane mataki kike tsakanin karatu da aiki?
Ina da digiri na farko daga Jami’ar Ahmadu Bello Zaryia ina kuma yin masters da nake a Jami’ar Baze da ke Abuja Unibersity Abuja, digiri na biyu. Bsc accounting shi ne digiri na farko.
Kina sana’a ne bayan aikin banki ko a’a?
Ba na sana’a ina tafiyar da kamfanina ne kuma ina yiwa mutane da yawa ‘consultancy’. Ni ba ‘yar kasuwa ba ce kamar yadda na ce ni tsohuwar ma’aikaciyar banki ce da na bari a matsayin manajar reshe.
Ga shi kin yi karatu da yawa kuma har kin shekara goma sha biyar kina aiki kika bari kuma kina da kamfani to me kike son cimma a rayuwa?
Ina so in yi taimako a rayuwata in taimaka ma al’umma ta hanyoyin fadakarwa, rubutu, da kuma ya zamanto na yi fice a harkar rubuce-rubuce na duniya da kuma a san ni ma’ana ina son in yi suna.
Ya ya sunan kamfanin naki kuma wane irin aiki kuke gudanar wa a cikinsa?
Sunan kamfanina Shawullam Nigeria Limited kuma ni ce MD/CEO (Mai kula da tafiyar da shi) ina da ma’aikata wadanda suke karkashina kuma ni nake biyan su albashi. Ayyukan da muke yi a kamfanin suna da yawa; kin ga muna yin Financial consultancy da management, Contracts and supplies (kwangila da sari), muna da reshen ruwan roba da muke da shi, ina kuma da reshen da muke fassara ayyuka daga Turanci zuwa Hausa ko Hausa zuwa Turanci. Na yi ayyukan fassara na littattafai biyu kuma an buga na Dakta Badamasi Shu’aibu Burji kamar haka; In so ya yi so wanda na fassara shi zuwa harshen Turanci ya koma ‘When Lobe reaches its peak money has no influence’ sai kuma A dalılin so zuwa ‘For the sake of lobe’ wanda na fassara zuwa harshen Turanci shi ma, an buga su ma duk a kamfanin Dakta Badamasi Burji.
Mene ne ya ja hankalinki kika fara rubutu kuma yaushe?
Na fara yin rubutu tun ina karama kuma ko a lokacin da nake aikin banki da safe zuwa dare ni ma’aikaciyar banki ce da tsakar dare kuma ina rubuce-rubucena, shi ya sa ko lokacin da na gama littafin Rakiba ina banki amma sai bayan da na bar banki na sake shi kasuwa. Kuma ina yawan karance-karance domin yanzu haka ina da collection na littattafan Turanci masu yawa sama da 5000, a dakin karatu na na musamman .
Ta yaya kika tsinci kanki a harkar rubutu?
Sha’awar rubutu kamar yadda na fada tun farko shi ne ya sa na tsinci kaina da kuma yawan karance-karance na, da bincike kuma da burin ni ma idan ina raye in ga sunana a kan bangon littafi. Yanzu haka ina da Rakiba mai shafuka 447 yayin da na Turanci da Hausa a kasuwa, Karima na Hausa mai shafuka 87 duk suna a kasuwa.
Wadanne irin sakonni kike son isarwa ga al’umma ta hanyar rubutu?
Ina son in isar da salo-salon sako a rubutuna domin kowane yana zuwa da darasi mai karfi da gamsarwa wadanda zasu amfani al’umma kuma idan aka sa su a (tsarin karatu) don makarantu ma sai a nusar da mai karatu yanayin zamantakewar rayuwa da bil’adama kala-kala a ayyukan da nake rubutawa domin irin sigar rubutuna ya fita daban da irin wadanda aka saba gani. Yanzu haka kamar yadda na fada maki ina kungiyoyin marubuta manya na Nijeriya da na kuma waje.
Ya sunan Kungiyoyin da kike ciki?
Shugaba kungiyar marubuta ta kasa da kasa (IWA), kungiyar marubuta mata ta kasa da kasa IWWG, sai kuma kungiyar matasan marubuta ta Nijeriya, duk wadannan manyan kungiyoyi ne na harkar marubuta.
Yare ko harshe nawa kike ji?
Yanzu haka ina jin Kanuri, Hausa da yaren Jamus (Jamusanci).
Wane abu ne aka taba yi miki a rayuwa wanda ba za ki taba mantawa da shi ba na farin ciki ko akasin haka?
Gaskiya suna da yawa amma a banki da aka bani award (kambu) na karramawa ta gwarzuwar shekaru biyu a jere.
Me yake sa ki farin ciki?
Kyautatawa da gaskiya da kuma rikon amana.
Me yake bata miki rai?
Munafinci da butulci da cin amana.
Me kika fi so a yi miki kyauta da shi?
Turare, littafi da jaka.
Tsakanin dare da rana wane lokacin ne kika fi so wajen gudanar da rubutunki?
Na fi son dare domin lokacin na fi samun nutsuwar kwakwalwa.
A yanayin gari wane irin yanayi kika fi so sanyi zafi ko lokacin bazara?
Lokacin sanyi da damina gaskiya na fi son su.
A cikin littattafan da kika rubuta wanne kika fi so?
Gaskiya duk ina son littattafai na amma Rakiba shi ne wand ana fi so shi ne littafina na farko a duniya.
Wanne rubutu ne ya ba ki wahala?
Gaskiya littafin da ya ba ni wahala shi ne littafin (Kaladeiscope) shi bai fito kasuwa ba tukun amma zan sake shi kafin karshen shekarar nan Insha’Allahu, shi ma na turanci ne.
Wace kala kika fi so?
Na fi son ja da shudi da pink (kalar shanshambale) su ne kalolina gaskiya.
Wane irin abinci kika fi so?
Gaskiya na fi son Spagetthi domin bana gajiya da ita daga safe har yamma ina kuma son masa da miyar ganye sannan ina son Danwake kuma..
Mene ne yake burge ki ga mutane?
Hali nagari da sanin mutuncin mutum da daraja shi.
Wane fata za ki yi ga LEADERSHIP Hausa?
Ina yi musu fatan alheri. Allah ya sa su fi haka su zama farin wata.