…shi ma da ya tofa nasa albarkacin bakin dangane da rash-in albashi mai tsoka, Olamide Alalade ya yi kira ga masu ruwa da tsaki wajen tafiyar da al’amuran ilimin daga kowane bangare, da su samar da albashi mai tsoka; wan-da zai iya magance matsalolin da malaman makaranta ke fuskanta na rayuwar a halin yanzu.
Alalade ya kara da cewa, akwai bukatar a kara mayar da hankali a kan makarantun da suke a kauyuka, birane da kuma sauran wuraren da ke makwabtaka da su. “
- Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya(2)
- Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (1)
Malaman da muke da su yanzu, na wucin-gadi ne; mu-samman a bangaren Turanci da Lissafi, hakan ne zai sa ba za mu taba hada tsakanin malaman da suke na dindindin da kuma na wucin-gadi ba, ko da kuwa a kwazon su kansu daliban; domin za su fi mayar da hankali idan suna da malamai na dindindin.
Me yasa muke da malaman wucin gadi a bangaren Tu-ranci da Lissafi a makarantu? Amma, sai ga shi muna ganin malamai da dama na neman koyarwa ta wucin ga-din, saboda irin wadannan malaman ba su da lokacin da za su bayar wajen taimaka wa daliban, su gane wuraren da suke da matsaloli; domin su gyara. Idann ana ma-ganar malaman wucin gadi, dole ne malamai su raba hankalinsu wajen suntiri daga wannan makaranta zuwa waccan makaranta, ko kuma su fara tunanin yin wata sa-na’a daban. Abu mafi kyau shi ne a samu malaman Lissa-fi da Turanci wadanda za su kasance a makaranta a kowane lokaci, domin taimaka wa ‘ya’yanmu dalibai wajen inganta iliminsu a cewar Alalade.
Yadda Makarantun Suka Bambanta
Bugu da kari, Alalade ya ce; yadda makarantu suka bam-banta kan lamuransu, na shafar irin hazakar da daliban suke da ita ko samu daga makarantun. Yayin da kuma wasu makarantu ke kallon irin ribar da za su samu, wasu kuma ilimin da daliban za su samu shi ne damuwarsu.
“Idan makarnta ta kasance ba ta da wasu muhimman lamuran da ta sa a gabanta, musamman na koyar da da-russa, sai ya kasance malaman za su mayar da hanka-linsu ne a kan wasu dalibai a cikin ajin kawai, su kuma manta da sauran. Mun kuma lura da cewa, idan yara ma-su zuwa makaranta suka karu, a nan ba ana nufin ana karuwa ba ne da ilimi.
Malamai kalilan ne, amma ana amfani da su wajen koya wa dalibai da dama karatu. Shin akwai wasu matakai ko kididdigar da ke nuna cewa, a duk shekara ga yawan wadanda suka karanta fannin koyarwa; wadanda za su tafiyar da irin bukatar da ake da ita a Nijeriya?
Abin ba haka yake ba, muna dai da makarantun da suka kasance wurin da ake amfani da malaman da ba su can-canta ba. Ba da dadewa ba, aka samu irin wannan lamari wanda ya dace a ce an dauki babban mataki, akwai kashi 50 na wadanda suka rubuta jarrabawar shiga manyan makarantu (Jamb), wadanda suka samu maki kasa da 200; saboda wasu makarantun na tafiyar da harkokin nasu ne kawai, don samun riba maimakon ganin daliban nasu na yin fice wajen samun nasarar jarabawar.
Kamata ya yi mu rika kaucewa kaskantar da samun ci gaban ilimi, saboda ba mu da wadanda suka cancanta su kasance a guraben da ake so. Kamata ya yi samar da mu-radin yin gyara, ba ya kasance jiya tafi yau ba. Mutane ba za su ga muhimmancin abin da aka yi watsi da shi ba!
Ba A Kallon Aikin Koyarwa Da Muhimmanci
A ganin Omisore, akwai bukatar kwarewa idan har ana maganar malamai masu nagarta, wadanda za su dora dalibai a tudun mun tsira na harkar koyon karatu.
“Ya ce, a ganinsa dalili na biyu shi ne yadda lamarin ko-yarwa ya lalace tare da tabarbarewa, daya daga cikin abubuwan da yake amfani da su a matsayin dabarun ho-rarwa, don samun nasarar aikin koyarwa da suka hada da A, B, C, D da E. A, malami ya tafiyar da kai a duk halin da ya samu kansa, B ya iya mu’amala da al’umma, C can-cantar yin aikin, D sanin hanyar koyarwar da ta dace, E sabo da aikin saboda yau da kulllum.
Cancanta ita ce tafi komai muhimmanci ga malami, mu-samman wajen cimma burin koyarwar, yawancin mala-mai ba sa bin hanyoyin da za su kara inganta kansu, daga karshe suna dora dalilin hakan a kan rashin albashi mai tsoka.
Dalili na uku, na da alaka da na daya da biyu, wanda gaba daya yana da nasaba da yadda aka yi wa lamarin rikon sakainar kashi, wato aikin koyarwa, saboda rashin can-canta da kuma yadda ake yi wa aikin koyarwar kallon masheka Aya. Haka nan, ma ana iya samun Kwalejin ilimi an cika ta da daliban da ba su samu damar cancanta a dauke su ba, ba domin komai ba sai saboda wadanda su-ka cancanci ba su da sha’awar lamarin da ya shafi ko-yarwa.