ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)

by Sulaiman and Idris Aliyu Daudawa
2 years ago
turanci

…shi ma da ya tofa nasa albarkacin bakin dangane da rash-in albashi mai tsoka, Olamide Alalade ya yi kira ga masu ruwa da tsaki wajen tafiyar da al’amuran ilimin daga kowane bangare, da su samar da albashi mai tsoka; wan-da zai iya magance matsalolin da malaman makaranta ke fuskanta na rayuwar a halin yanzu.

Alalade ya kara da cewa, akwai bukatar a kara mayar da hankali a kan makarantun da suke a kauyuka, birane da kuma sauran wuraren da ke makwabtaka da su. “

  • Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya(2)
  • Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (1)

Malaman da muke da su yanzu, na wucin-gadi ne; mu-samman a bangaren Turanci da Lissafi, hakan ne zai sa ba za mu taba hada tsakanin malaman da suke na dindindin da kuma na wucin-gadi ba, ko da kuwa a kwazon su kansu daliban; domin za su fi mayar da hankali idan suna da malamai na dindindin.

ADVERTISEMENT

Me yasa muke da malaman wucin gadi a bangaren Tu-ranci da Lissafi a makarantu? Amma, sai ga shi muna ganin malamai da dama na neman koyarwa ta wucin ga-din, saboda irin wadannan malaman ba su da lokacin da za su bayar wajen taimaka wa daliban, su gane wuraren da suke da matsaloli; domin su gyara. Idann ana ma-ganar malaman wucin gadi, dole ne malamai su raba hankalinsu wajen suntiri daga wannan makaranta zuwa waccan makaranta, ko kuma su fara tunanin yin wata sa-na’a daban. Abu mafi kyau shi ne a samu malaman Lissa-fi da Turanci wadanda za su kasance a makaranta a kowane lokaci, domin taimaka wa ‘ya’yanmu dalibai wajen inganta iliminsu a cewar Alalade.

Yadda Makarantun Suka Bambanta

LABARAI MASU NASABA

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

Bugu da kari, Alalade ya ce; yadda makarantu suka bam-banta kan lamuransu, na shafar irin hazakar da daliban suke da ita ko samu daga makarantun. Yayin da kuma wasu makarantu ke kallon irin ribar da za su samu, wasu kuma ilimin da daliban za su samu shi ne damuwarsu.

“Idan makarnta ta kasance ba ta da wasu muhimman lamuran da ta sa a gabanta, musamman na koyar da da-russa, sai ya kasance malaman za su mayar da hanka-linsu ne a kan wasu dalibai a cikin ajin kawai, su kuma manta da sauran. Mun kuma lura da cewa, idan yara ma-su zuwa makaranta suka karu, a nan ba ana nufin ana karuwa ba ne da ilimi.

Malamai kalilan ne, amma ana amfani da su wajen koya wa dalibai da dama karatu. Shin akwai wasu matakai ko kididdigar da ke nuna cewa, a duk shekara ga yawan wadanda suka karanta fannin koyarwa; wadanda za su tafiyar da irin bukatar da ake da ita a Nijeriya?

Abin ba haka yake ba, muna dai da makarantun da suka kasance wurin da ake amfani da malaman da ba su can-canta ba. Ba da dadewa ba, aka samu irin wannan lamari wanda ya dace a ce an dauki babban mataki,  akwai kashi 50 na wadanda suka rubuta jarrabawar shiga manyan makarantu (Jamb), wadanda suka samu maki kasa da 200; saboda wasu makarantun na tafiyar da harkokin nasu ne kawai, don samun riba maimakon ganin daliban nasu na yin fice wajen samun nasarar jarabawar.

Kamata ya yi mu rika kaucewa kaskantar da samun ci gaban ilimi, saboda ba mu da wadanda suka cancanta su kasance a guraben da ake so. Kamata ya yi samar da mu-radin yin gyara, ba ya kasance jiya tafi yau ba. Mutane ba za su ga muhimmancin abin da aka yi watsi da shi ba!

 

Ba A Kallon Aikin Koyarwa Da Muhimmanci

A ganin Omisore, akwai bukatar kwarewa idan har ana maganar malamai masu nagarta, wadanda za su dora dalibai a tudun mun tsira na harkar koyon karatu.

“Ya ce,  a ganinsa dalili na biyu shi ne yadda lamarin ko-yarwa ya lalace tare da tabarbarewa, daya daga cikin abubuwan da yake amfani da su a matsayin dabarun ho-rarwa, don samun nasarar aikin koyarwa da suka hada da A, B, C, D da E. A, malami ya tafiyar da kai a duk halin da ya samu kansa, B ya iya mu’amala da al’umma, C can-cantar yin aikin, D sanin hanyar koyarwar da ta dace, E sabo da aikin saboda yau da kulllum.

Cancanta ita ce tafi komai muhimmanci ga malami, mu-samman wajen cimma burin koyarwar, yawancin mala-mai ba sa bin hanyoyin da za su kara inganta kansu, daga karshe suna dora dalilin hakan a kan rashin albashi mai tsoka.

Dalili na uku, na da alaka da na daya da biyu, wanda gaba daya yana da nasaba da yadda aka yi wa lamarin rikon sakainar kashi, wato aikin koyarwa, saboda rashin can-canta da kuma yadda ake yi wa aikin koyarwar kallon masheka Aya. Haka nan, ma ana iya samun Kwalejin ilimi an cika ta da daliban da ba su samu damar cancanta a dauke su ba, ba domin komai ba sai saboda wadanda su-ka cancanci ba su da sha’awar lamarin da ya shafi ko-yarwa.

turanci
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
turanci
Idris Aliyu Daudawa
+ posts Bio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Rayuwar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kyamar Baƙi: An Sake Kwaso Ƴan Nijeriya 83 Daga Afirka Ta Kudu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 60 Da Kayan Aiki A Edo
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tsohon Shugaban Ƙasa Jonathan Ya Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Ƙasa 18 A Jihar Bauchi

MASU ALAKA

turanci
Ilimi

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

August 31, 2026
turanci
Ilimi

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

August 29, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Ilimi

Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka

July 11, 2026
Next Post
Peng Liyuan Ta Yi Kira Da Karin Hadin Gwiwa Tsakanin Kasa Da Kasa Domin Takaita Cututtukan Kanjamau Da Tarin Fuka

Peng Liyuan Ta Yi Kira Da Karin Hadin Gwiwa Tsakanin Kasa Da Kasa Domin Takaita Cututtukan Kanjamau Da Tarin Fuka

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.