Majalisar Dokokin Jihar Kano ta shiga kika-ƙaƙa a lokacin da Kakakin Majalisar, Jibril Isma’il Falgore, ya kira tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, a matsayin muƙaddashin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa yayin da yake aike wa da saƙon ta’aziyya ga matar Ganduje, Farfesa Hafsat Ganduje, kan rasuwar mahaifiyarta.
Wannan kiran ya haifar da muhawara mai zafi, musamman daga Shugaban Marasa Rinjaye, Labaran Abdul Madari, da wasu ‘yan majalisar APC, waɗanda suka ce Ganduje ya kamata a kira shi da cikakken shugaban jam’iyyar, ba muƙaddashi ba.
- Sarakunan Da Ganduje Ya Nada Tamkar Kwamishinoni Ne – Shugaban NNPP
- Har Yanzu Tukunyar Rikicin Masarautar Kano Na Tafarfasa
Saboda wannan saɓani, zaman majalisar ya kasance an ɗage shi har zuwa ranar Talata.
Wannan zaman ya kasance na farko tun bayan da majalisar ta dawo daga hutun kwanaki 48. Hutun ya biyo bayan zartar da dokar soke masarautu biyar a Jihar Kano, inda jinkirin dawowar ke da nasaba da matsalolin tsaro da suka taso bayan wannan muhimmin sauyin dokar kamar yadda jaridar Nigerian Tracker smta rawaito.