A wani gagarumin yunkuri na shawo kan matsalar karancin abinci, gwamnatin tarayya ta kaddamar da rabon shinkafa tirela 740 a fadin Nijeriya.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnatin jihar bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya da shugaban kasa Bola Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin.
- Sojojin Sama Sun Yi Lugudan Wuta Kan Ƴan Ta’adda A Kaduna
- Sufeta Janar Na Ƙasa Ya Dakatar Da Aiwatar Da Na’urar E-CMR Bayan Shan Suka
Kowacce daga cikin Jihohi 36 na Tarayya da Babban Birnin Tarayya (FCT) za ta karbi tirela 20 na shinkafa, inda kowace tirela ke dauke da buhuna kusan 1,200 (25kg).
Wannan ya kai kusan buhunan shinkafa 24,000 a kowace jiha, wanda za a rabawa marasa galihu.
Ministan ya nemi Gwamnonin Jihohin da su yi tsari mai kyau ta yadda rabon zai isa ga masu tsantsar bukata