Gwamnatin Tarayya ta kwaso jumlar ‘yan Nijeriya 190 da suka makale a Hadaddiyar Daular Larabawa zuwa gida.
A cewar sanarwar da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta fitar mai dauke da sa hannun babban daraktanta mai kula da shiyar arewa ta tsakiya, Bashir Garga, a yau Talata, ta ce ayarin jami’an gwamnati karkashin jagorancin NEMA sun tarbi mutanen da suka dawo gidan a filin saukar jiragen saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja da misalin karfe 5 da mintuna 57 na asuba.
- Kotu Ta Yi Watsi da Buƙatar Emefiele Na Tafiya Birtaniya Duba Lafiyarsa
- Dan Majalisar Tarayya Ekene Daga Kaduna Ya Rasu
NEMA ta kara da cewar hukumomin daya kamata sun dauki bayanan mutanen, tare da jan hankalinsu akan “zama mutane na gari” bayan da suka dawo Nijeriya.
“Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan Nijeriya, su zamo jakadun kasar nan na gari, tare da dabbaka akidun kishin kasa da bin doka da oda da zama sahihan mutane masu mutunci.”
Idan za’a tuna, a watan Oktoban 2022, gwamnatin tarayya ta dawo da jimillar mutane 542 gida daga Hadaddiyar Daular Larabawa.