Mutum 15 ne a hukumance suka rasa rayukansu yayin da aka kammala jigilar alhazan Nijeriya 51,000 zuwa gida daga Makkah.
Da yake bankwana da sauran jami’an hukumar NAHCON a ofishin hukumar a Makkah, shugaban hukumar, Jalal Ahmad-Arabi, ya ce hukumar ta fara duba irin kalubalen da aka samu a farko bisa rashin daidaiton canjin Naira zuwa dalar Amurka.
- Talauci Da Rashin Aikin Yi Ne Ke Kara Yawaitar Masu Zamba Ta Yanar Gizo – Masani
- Southgate Ya Ajiye Aikin Horas Da Ingila
Ya yi fatan yin sabon shiri da wuri don fuskantar aikin hajjin 2025 ta hanyar magance matsalolin da aka fuskanta a bana.
“Da gaske ne an fara tangal-tangal abun kamar ba za ta mike ba amma da yake mun yi tsayin-daka tun a na mutum a’a dubu goma dubu ashirin dubu 51 suka zo ta fannin gwamnati.”
Babban likitan alhazan, Dokta Abubakar Adamu Isma’il, ya yi bayanin alkaluman da aka tattara bayan kammala aikin hajjin na wadanda a ka rasa inda ya tabbatr cewa “Jimillar gaba daya idan aka hada da Madina da Makkah da Masha’ir mutum 15 kenan.
“Idan ka tuna lokacin da muka kira taron manema labarai kafin Arafat mutum 12 yanzu ga an samu uku” in ji likitan.
Ya kara da cewa cikin wadanda su ka rasu har da matar nan da ta fado daga gidan sama a Madina.