Gwamnatin Jihar Kano ta soke rabon filayen da tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi, waɗanda suke tsakanin Kwalejin Fasaha ta Jihar Kano da Kwalejin nazarin Shari’a ta Aminu Kano. Kwamishinan ƙasa da tsare-tsaren Jiki, Abduljabbar Umar, ne ya sanar da soke rabar da filayen, inda ya yi amfani da ikon da Gwamna Abba Yusuf ke da shi a ƙarƙashin sashe na 28 na dokar amfani da Ƙasa, shafi na 15 na dokokin Tarayyar Nijeriya na shekarar 2004.
Gwamnatin jihar ta sake mallakar sabon wurin a Badume, ƙaramar hukumar Bichi, da gwamnatin ta bayar a matsayin madadin fili.
Kwamishina Umar ya shaida cewa bayan kama aiki a ranar 29 ga Mayu, 2023, Gwamna Yusuf ya umarci a gudanar da ayyukan kula da ci gaba a filin da ake taƙaddama akai.
- Abba Ya Sake Nada Tsohon Sarkin Gaya Da Wasu Sabbin Sarakuna A Kano
- Hasashen Ambaliyar Ruwa A Kano: Wane Shiri Gwamnati Da Jama’ar Gari Suka Yi?
Ya jaddada cewa bayan bin duk hanyoyin da suka dace, an tabbatar da cewa rabon filin da aka yi a baya ya kasance ba bisa ƙa’ida ba. Saboda haka, gwamnati ta yi amfani da ikonta na doka don soke rabon filayen tare da mayar da filin ga Kwalejin Nazarin Shari’a ta Aminu Kano.
A cikin aiwatar da waɗannan ikon, Kwamishina Umar, wanda ke aiki a ƙarƙashin ikon da gwamna ya ba shi, ya sanar da jama’a cewa dukkan filin da ke ƙarƙashin lamba TPNUPDA/366 an mayar da shi ga Kwalejin Nazarin Addinin Musulunci ta Aminu Kano.