Gwamnatin Tarayya na shirin gabatar da sabon tsarin karatu ga dukkanin makarantun sakandare a fadin kasar nan a watan Satumban 2024.Â
Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne, ya sanar da hakan ga hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare (JAMB).
- Gwamnan Kano Ya Kwace Filayen Makarantun Da Ganduje Ya Cefarnar
- Shugaban Amurka, Joe Biden Ya Kamu Da Cutar Covid-19
“Muna aiki tukuru don tabbatar da cewa an gabatar da sabon tsarin karatu na makarantun sakandare a watan Satumba,” in ji Mamman.
Ya yi nuni da cewa, an fara aikin ne a shekarar da ta gabata kuma za a gudanar da taron masu ruwa da tsaki a ranar 6 ga watan Agusta, 2024 kan sabon tsarin karatun.
“Za a aiwatar da wannan tsari a dukkanin makarantun gwamnati da masu zaman kansu,” in ji Ministan.
A baya-bayan nan, Hukumar Ilimi ta Sakandare ta Kasa, ta yi Allah wadai da halin da manyan makarantun sakandaren kasar nan ke ciki, tare da yin kira da a hada kai don shawo kan wasu kalubalen da ke tattare da ilimi a kasar nan.
Hukumar ta lissafa wasu kalubale da fannin ilimi ke fuskanta, da suka hada da karancin kayan koyarwa, nagartattun malamai, tsofaffin manhajoji, dakunan karatu da dakunan gwaje-gwaje.