Rundunar sojin Nijeriya ta ce ta kubutar da wasu ‘yan mata biyu da ‘yan ta’addar Boko Haram suka yi garkuwa da su a makarantar sakandaren ‘yan mata ta gwamnati a garin Chibok da ke jihar Borno a shekarar 2014.
LEADERSHIP ta tattaro cewa ‘yan matan biyu da aka bayyana sunayensu da Hannatu Musa da Kauna Luka, Sojojin Birgediya 21 na sulke ne a karamar hukumar Bama a ranar 26 ga watan Yuli, suka ceto shekaru takwas bayan sace su.
- Jami’ar MAAUN Ta Rantsar Da Sabbin Dalibai Sama Da 500 A Kano
- ‘Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Gidaje Da Dama A Kaduna, Suna Sace Jama’a
A cewar wani rahoton sirri da aka samu daga manyan majiyoyin soji na Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya da kuma tsaro a tafkin Chadi, ya shaida wa wakilinmu, ‘yan matan sun tsere daga sansanin Gazuwa, hedikwatar kungiyar Jama’at Ahl-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, kungiyar Boko Haram, wadda a da ake kira Gabchari, Mantari da Mallum Masari, da ke da nisan kilomita tara zuwa garin Bama.
LEADERSHIP ta ce wasu ‘yan matan makarantar Chibok guda biyu da aka ceto a baya sun shaida wa hukumomin sojin cewa akwai ‘yan matan makarantar Chibok kusan 20 da har yanzu ake tsare da su kuma aka yi musu auren dole a sansanin Gazuwa.
‘Yan matan makarantar Chibok guda biyun da sojoji suka ceto a baya-bayan nan sune Mary Dauda da Hauwa Joseph.
Sai dai tserewar da suka yi daga sansanin ‘yan ta’addan ya biyo bayan gagarumin farmakin da dakarun ‘Operation Hadin Kai’ suka ci gaba da kai wa wanda ya janyo yunwa ya kuma sa ‘yan ta’addan yin kaura daga yankunan.
Idan za a iya tunawa kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da dalibai mata 276, masu shekaru daga 16 zuwa 18 a makarantar sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a ranar 14 ga Afrilu, 2014.
Sama da ‘yan matan makarantar 100 ne har yanzu ba a gansu ba.