Matakin Shugaban kasa, Bola Tinubu na kirkiro ma’aikatar bunkasa harkokin kiwo na ci gaba da janyo zafafan muhawara a tsakanin masu ruwa da tsaki.
Ko da yake, wani Lauya mai suna Madubuachi Idam, na kallon yunkurin na Tinubu a matsayin asara, domin akwai wasu ma’aikatun da ke da manufa irin aikin da wannan za ta yi, yayin da kuma kungiyar ci gaban matasan arewa (AYCF) da Afenifere da kuma Ohanaeze Ndigbo da suke da amannar wannan yunkurin abu ne mai kyau da zai iya kawo karshen matsalolin da ake samu tsakanin manoma da makiyaya.
- Gwamnan Kano Ya Kwace Filayen Makarantun Da Ganduje Ya Cefarnar
- Rikicin Sarautar Kano: Yadda Gwamnatin Abba Ta Sauya Alkibla
Tinubu ya kirkiri ma’aikatar ne da nufin kawo karshen rigingimun da ake samu a tsakanin manoma da makiyaya da kuma ganin an inganta harkokin da suka shafi kiwo a fadin kasar nan.
Tun da farko dai, Tinubu ya kafa kwamiti bayan da ya amshi rahoton yadda za a bunkasa harkokin kiwon a kasar nan, wanda Abdullahi Ganduje ya jagoranta, kuma kwamitin ya gabatar da rahotonsa watanni goma da suka gabata da ya bayar da shawarar samar da ma’aikatar.
Sama da shekaru dai an jima ana samun rigingimu a tsakanin manoma da makiyaya wanda hakan ya janyo asarar rayuka da dukiyoyin da ba za su misaltu ba.
Jihohi kamar su Filato, Benuwai, Kaduna, Inugu, Imo, Delta, Oyo da wasu jihohin na daga cikin wuraren da aka fi samun wadannan matsalolin.
Sai dai Tinubu ya ce, ta hanyar samar da sabuwar ma’aikatar za a samu nasarar dakile wannan matsalar. Ya nuna cewa, shiga gonakai a yi barna da kuma toshe wa dabbobi hanyoyin kiwo duk za su samu sauki kuma za a samu rage asarar abinci da rage kaIfin matsaloli ta wannan ma’aikatar.
Sai dai Lauya Madubuachi Idam, ya soki lamarin da cewa an kirkiro ma’aikatar ne domin asarar dukiya a daidai lokacin da jama’an kasa ke kukan talauci da fatara.
Ya ce a maimakon hakan, kamatuwa ya yi a maida hankali kan ma’aikatar gona wanda za ta iya shawo kan lamuran da suka shafi kiwo ba wai sake kirkiro wata ma’aikata don bata kudin kasa ba.
Shi kuma a bangarensa, shugaban kungiyar ci gaban matasan arewa AYCF, Yerima Shettima, ya ce, kirkiro wannan ma’aikatar da Tinubu ya yi tabbas abun a jinjina masa ne kuma yanzu na da abun da zai iya bugan kirji ya nuna wa ‘yan Nijeriya cewa ya yi.
Shettima, ya yi fatan cewa ma’aikatar za ta samu nasarar kawo karshen rigingimun da ake samu a tsakanin manoma da makiyaya, duk da ya misalta matakin a matsayin abun murna matuka.
Ya ce, “Mun yi murna sosai da muka ji labarin an samar da ma’aikatar kula da lamuran kiwo wannan na nuni da cewa gwamnatin nan na da abun da za ta nuna wa ‘yan Nijeriya cewa ta yi wajen ganin ta kawo karshen rikicin manoma da makiyaya.”
Ita ma kungiyar Fulanin ta MACBAN ta bakin daraktan yada labaranta reshen Jihar Kaduna, Ibrahim Bayero Zango, ya ce, tabbas ma’aikatar za ta share hawayen matsalolin da suke akwai kuma za ta kawo mafita ga rikicin manoma da makiyaya.
Zango ya sanya kafa ya shure ikirarin da ke cewa kirkirar ma’aikatar bata kudi ne kawai. Ya ce, ko da wasa ba asarar kudi za a yi ba, illa daura kasar zuwa turbar ci gaba.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan lamarin, darakta janar na kungiyar Ohanaeze, Okechukwu Isiguzoro, ya ce, ma’aikatar za ta shiga tsakanin rikicin manoma da makiyaya da kuma kawo mafita ta karshe, don haka ne suka jinjina wa samar da ma’aikatar.
Haka su ma kungiyar ci gaban al’ummar Yarbawa, Afenifere, ta ce dukkanin wani yunkurin da zai kawo karshen kai hare-haren tsakanin manoma da makiyaya abun yabawa ne kuma tabbas suna goyon bayan wannan yunkurin.
Kakakin kungiyar, Kwamarat Jare Ajayi, ya ce, ba su kallon matakin na Tinubu a kokarin fifita wani yanki ko wata kabila, illa wani mataki da zai kawo karshen matsalolin manoma da makiyaya. Ya nuna cewa ana samun matsalar rikicin manoma da makiyaya a kowani sassa na kasar nan, don haka ba wata kabila ko zallar yanki ne za su mori wannan ma’aikatar ba, illa dukkanin kasar ce za ta mora.