Gusau ita da wasu wuraren da suke makwabtaka da ita an mika su ga Mallam Sambo Dan Ashafa sun kasance ne a cikin birnin na masarautar.A Gusau bayan ta kasance karkashin Mallam Sambo da hedikwatarta take a Gusau tana da wasu garuruwa da suke har ila yau karkashin Wonaka, Mada, Yandoto, Samri, Magami, Marabu, Mareri, Mutumji, Kwaren Ganuwa, Wanke da wasu kauyukan da suke zagaye da Gusau, kamar sauran sassan na daular Usumaniyya.
Ta hanyar lamarin tafiyar da mulki bayan da akwai wadanda suke taimakawa ita Gusau din wajen tafiyar mulki, har ila yau sai unguwanni biyar, bayan da aka kasa shi garin Gusau din zuwa unguwanni ko shiyya kamar yadda sunayen su suke haka,Shiyyar Magaji, Uban Dawaki, Galadima, Mayana da kuma Sarkin Fada. Sune suke wata kafa da take sada al’umma tsakaninsu da Dagatai ko masu unguwanni,da kuma Sarkin katsinan Gusau (Emir Of Gusau).Su ne suka kasance kunnuwa da kuma idanun Sarki.Gusau kamar sauran sassan da suke karkashi daular Usumaniyya suna aikawa da kason fadar Sarkin musulmi na irin kudaden da ta samu.
- Rikicin Masarautar Kano: Tinubu Da Sanusi II Suna Da Alaka Mai Karfi – Fadar Shugaban Kasa
- Har Yanzu Tukunyar Rikicin Masarautar Kano Na Tafarfasa
Bayyanar mulkin mallaka na Turawa ya kawo nau’oin cigaba na garin Gusau da kungiyoyin da suke cikin birnin. Abubuwan more rayuwa kamar hanyoyi da aka sa ma kwalta, hanyar jirgin kasa, manyan kantuna, da wasu harkoki, manyan kamfanoni duk an kawo ma shi birnin da haka ne kuma Gusau ta kara samun bunkasa ta cigaban zamani.
Sai dai duk da haka wasu tsare- tsaren mulkin mallaka da aka kawo sune suka sauya salo na mulkin.Idan ba haka b agarin na Gusau bai kai a rika ba shi girma da daukaka ba, amma sai ga shi cikin kankanen lokaci lamurra sai suka canza.Lokacin mulkn mallaka na turawa ne aka fa amsar harajin dabbobi a shekarar 1907 da ake kira da suna (Jangali).
Zamanin mulkin mallakar ne sana’ar noma ta kasance babbar abar da take bunkasa tattalin arziki na garin Gusau,abin kuma sai ya kara bunkasa garin ya kasance na manoma.Sana’ar noma ta zama ba tad ana biyu idan ana maganar tattalin arziki ne wadda ake yi da Damina wajen noma kayan amfanin gona a ci da kuma sayarwa
Jerin Sunayen Sarakunan Gusau
Malam Sambo Dan Ashafa 1806- 1827
Wadannan Sarakunan shida na daga cikin zuri’ar Sambo Dan Ashafa kamar haka:
Malam Abdulkadir 1827-1867
Malam Muhmmadu Modibbo 1867-1876
Malam Muhammad Tuburi 1876-1887
Malam Muhammadu Gide 1887-1900
Malam Muhammadu Murtala 1900-1916
Malam Muhammadu Dangida1916-1917
Sai dai kuma daga shekarar 1917 zuwa 1984 ba a bayyana sunayen Sarakunan da ba.
Alhaji Muhammadu Kabir Danbaba Sarkin Katsinan Gusau 1984- 2015
Alhaji Ibrahim Bello 2015 zuwa yanzu.