A kokarin da shugaban hukumar fina-finai ta Nijeriya, Ali Nuhu yake yi wajen ganin masana’antar Fim ta ci gaba da tsayuwa da kafafunta, ya yi wani zama da masu ruwa da tsaki a kan masana’antar Kannywood da gidajen sinima a arewacin Nijeriya domin zakulo hanyoyin da ya dace abi wajen dawo da martabar gidajen sinima a arewacin Nijeriya.
Ali Nuhu ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa “Yin hulda tare da masu ruwa da tsaki na Kannywood, masu gidajen sinima, da hukumomin gudanarwa a yau ya kasance abin farin ciki da haske.
- Hasashen Ambaliyar Ruwa A Kano: Wane Shiri Gwamnati Da Jama’ar Gari Suka Yi?
- Rikicin Sarautar Kano: Yadda Gwamnatin Abba Ta Sauya Alkibla
Mun magance matsalolin da ke addabar gidajen sinima a Arewa, inda muka binciko hanyoyin shawo kan kalubalen da share fagen ci gaba.
Kamar yadda ba a kwana daya aka gina kasar Rome ba haka zalika da sannu hakar mu za ta cimma ruwa a wannan aiki da muko dauko, amma kokarin hadin gwiwarmu ba shakka zai haifar da ingantaccen filin wasan kwaikwayo.
Bayyanar sabbin gidajen sinima irin su Silberbird da Ded Cinema a Kano, Kaduna, da Katsina, tare da wadanda ake da su irin su Platinum a Kano, Cinema Fasnet a Yola, da Canal a Maraba, na nuna kyakkyawar makoma.
Wadannan abubuwan da suka faru suna bayyana yiwuwar yankin na zama cibiyar masu sha’awar fina-finai a Nijeriya ta inda za su samar da duk wani abu domin ci gaba wannan harka kama daga jarumai, wajen aiki da sauransu.
Tattaunawar tamu ta jaddada kudirinta na tallafawa da ciyar da harkar fim gaba a Arewacin Nijeriya, ta hanyar yin aiki hannu da hannu domin mafarkinmu da kuma mafarkin sinima ya zama gaskiya, duwa yanzu komai ya kankama kuma akwai alamun nasara a gaba muddin muka cigaba da hada hannu domin gudanar da wannan aiki”.