Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya ce babu wata hanyar da za a bi wajen magance karancin mai da ya dabaibaye harkar sufurin jiragen sama a Nijeriya.
Ministan ya bayyana haka ne bayan wani taron gaggawa da ya yi da kungiyar ma’aikatan jiragen sama ta Nijeriya (AON) jiya a Abuja.
- Buhari Ya Nada Dakta Suleiman Umar Shugaban KADPOLY
- Rashin Tsaro: Ba Wani Abun Mamaki Idan ‘Yan Bindiga Suka Sace Buhari – Buba Galadima
Ya ce babu wata mafita a yanzu saboda kalubalen da ke tattare da matsalar ta shafi duniya ne baki daya.
A cewarsa, “Karancin makamashin ya shafi duniya ne gaba daya. A yau akwai matsalar man jiragen sama a duk duniya. Daga Amurka zuwa New Zealand. Ya ta’azzara a Nijeriya saboda ba mu yi shirin samar sa ishasshen mai ba.
Hakan kuma ya kara ta’azzara saboda kudaden kasashen waje ba su da yawa a Nijeriya saboda yadda ake samun kudin waje ma ya ragu.”
Ya kuma bayyana cewa a baya gwamnatin tarayya ta samar wa kamfanonin jiragen sama da tan 10,000 na man jiragen sama, kuma gwamnati na son kara yin hakan.
Idan za a iya tunawa tsadar man jiragen sama ta haifar da hauhwar farashinsa, lamarin da ya sanya fasinjoji rage amfani da jiragen.
Wasu kamfanonin jiragen sama sun yi barazanar daina sufuri saboda karanci da kuma tsadar da man jiragen ke yi.