Fitaccen mai fashin baki a kan al’amuran yau da kullum a Nijeriya, Adamu Abubakar ya danganta kalaman batanci da wani ya yi a kan gawurtacciyar matatar man fetur ta Dangote a matsayin abin da zai shafi makomar ‘yan kasuwa masu tasowa a Nijeriya da kuma na nahiyar Afirka.
A cikin wata sanarwa da Adamu ya rabawa manema labarai ya ce, furucin suki burutsu ne kawai kuma ya yi hakan bisa wata manufar da ba zai ci nasara ba.
- Na Fi Fifita Kishin Ƙasa A Kan Tara Riba – Dangote
- Jakadar Sin A Nijar Ya Halarci Bikin Bude Gasar Dambe Ta Nijar Karo Na 6
A cewarsa, furuncin l Babu gaskiya a cikinsa inda ya yi nuni da cewa, furucin wani yunkuri ne salon yiwa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa wanda kuma ya yi daidai da cin amanar kasa.
Adamu ya ci gaba da cewa, ga ‘yan kasuwa masu tasowa a Nijeriya da wadanda ke Afirka, matatar Mai ta dangote, tamkar wata alama ce da za ta kara musu karsashi don son cin nasara a kasuwanci su.
Ya ce, furucin wani yunkuri ne na son yi wa dimbin ‘yan Nijeriya bakin ciki musamman don su samu aikin yi a matatar man.
A karshe, Adamu ya sanar da cewa, matatar man ta Dangote, ta kasance sama da masana’antar aiki, amma masana’anta ce da za ta samar wa da ‘yan Nijeriya da ‘yan Afirka alkibla mai dorewa da kuma samar musu da ci gaba ta bangarori da dama.