An tara wa kamfe din yakin neman zaben takarar shugabar kasar Amurka, Kamala Harris fiye da dala miliyan 49 da dubu 600 tun bayan da Shugaba Joe Biden ya sanar da dakatar da kamfe dinsa.
“Tun bayan da shugaban kasa ya nuna goyon bayan ga mataimakiyarsa Harris a jiya da rana, Amurkawa sun bai wa yakin neman zabenta gudun muwar dala miliyan 49.6,” in ji kakakin Biden.
- Gwamnatin Matawalle Ce Ta Rura Wutar Ta’addanci A Arewa – Turji
- Jihar Kano Na Shirin Gudanar Da Zaben Ƙananan Hukumomi – Gwamna Abba
A jiya da daddare, dubban Amurkawa bakar fata a Amurka ne suka yi wata tattaunawa a manhajar Zoom inda suka nuna goyon bayansu ga ‘yar takarar.
Kungiyar ‘Win With Black Women’ ce ta shirya taron kuma ta tara fiye da dala daya da rabi a cikin sa’o’i uku.
Kungiyar ta ce mata fiye da dubu 44 ne suka halarci taron ta manhajar Zoom.