Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya amsa tambayoyin da manema labarai suka gabatar, don gane da ko Sin da Philippines sun cimma matsaya daya kan ikon mallakar sashin tudun ruwa na Ren’ai, inda ya ce tabbas sashin tudun wani bangare ne na tsibirorin Nansha, kuma Sin na da ikon mallakar wadannan tsibirai, da sararin tekunsu, ciki hadda tudun ruwa na Ren’ai.
Kaza lika, Sin kuma ta gabatar da ka’idoji uku kan yadda za a daidaita batun:
Na farko, jirgin ruwan yaki da kasar Philippines ta girke a wurin ya keta ikon mulkin mallakar Sin, kuma ya sabawa sanarwar ayyukan bangarori daban-daban dake shafar batun tekun kudancin Sin, musamman ma aya ta 5, wato haramta zama ko gudanar da ayyuka a sassan tudun ruwa da babu mazaune. Sin ta nemi Philippines da ta janye jirginta daga wurin, don maido da yanayin tudun ruwa na Ren’ai yadda ya kamata.
Na biyu, kafin Philippines ta janye wannan jirgi saboda dalilin jin kai, idan akwai bukatar samarwa ma’aikatan jirgi tallafin kayayyakin zaman rayuwa, ya kamata tun da farko Philippines ta nemi izni daga bangaren kasar Sin, idan Sin ta tantance bukatar, Philippines na iya samar da kayayyakin karkashin sanya idon Sin.
Na uku, Sin ba za ta amince Philippines ta yi sufurin manyan kayayyakin gine-gine zuwa wurin da nufin inganta jirgin har ya zama wata tashar sintiri ta dindindin ba. Har ila yau Sin za ta dauki matakan da suka wajaba don hana aukuwar lamarin, don kiyaye ikon mallakar yankunan kasa, da sanarwar gudanar da harkoki ta bangarorin da suke shafar tekun kudancin Sin.
Sau da dama kasar Sin ta gudanar da shawarwari da zaman sulhu da bangaren Philippines a kwanakin baya bisa wadannan ka’idoji 3, tare da kaiwa ga shirin wucin gadi na samar da kayayyakin yau da kullum ga ma’aikatan jirgin ruwan bisa manufar jin kai. Bugu da kari, bangarorin biyu sun kai ga cimma matsaya daya game da daidaita bambancin ra’ayi a kan teku, da gaggauta kwantar da hali game da halin da ake ciki a tekun kudancin Sin. (Amina Xu)