A kwanakin baya ne, gwamnatin tarayya ta shelanta cewa; ta amince da shigo da abinci cikin kasar nan daga kasashen ketare, har na tsawon kwanaki 150; ba tare da biyan ko sisin kwabo a matsayin haraji ba.
Har ila yau, kayan abincin da gwamnatin ta amince a shigo da su din sun hada da; Masara, Shinkafa, Alkama da sauran makamantansu, wanda ta ce; ta dauki wannan mataki ne, domin dakile hauhawar farashin kayan abinci a dukkanin fadin wannan kasa baki-daya, kamar yadda Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Samar da Wadataccen Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya shaida wa manema labarai a Abuja.
- Nijeriya Da Amurka Sun Jaddada Kudurin Karfafa Kasuwanci A Tsakaninsu
- Gwamnatin Kano Ta Sayi Taki Tirela 180 Domin Bunkasa Noma A Jihar
Sai dai kuma, wakilinmu ya ji ta bakin wasu masu ruwa da tsaki wadanda kuma manoma ne a kan wannan batu, inda akasarinsu suka nuna cewa, gwamnatin ta riga ta baro shiri tun rani.
Haka zalika, daya daga cikinsu; Alhaji Adamu Makarfi, Shugaban Manoman Masara na Arewa Maso Yamma; a hirarsa da LEADERSHIP Hausa ya bayyana cewa, wannan mataki; ko kadan ba zai haifar wa da Nijeriya da mai Ido ba, domin kuwa kamata ya yi bayan an zabi Shugaba Tinubu a matsayin shugaban kasa; ya ayyana dokar ta baci a fannin aikin noma, musamman ta fuskar magance kalubalen rashin tsaro, duba da yadda ake kashe manoma a Arewacin wannan kasa babu ji babu gani. Haka zalika, kyautuwa ya yi a ce ya wanzar da kudurinsa na magance kalubalen rashin tsaron, ta yadda ‘yan kasa za su gani a kasa, ba kawai kuma sai a siyasantar da fannin ba; da sunan daukar matakin shigo da abinci ba tare da biyan haraji ba, domin duk kasar da aka ce babu abinci, ko shakka babu za ta kasance cikin babbar fitina da halin dardar.
Makarfi ya ci gaba da cewa, akasari tun kafin zuwan wannan gwamnati, ana sayar wa da manoma takin zamani ne a kurarren lokaci; sannan kuma da matukar tsada duba da yadda kusan a bana, aka sayar da takin zamanin a kan kusan farashin Naira 40,000 duk buhu guda, wanda hakan ke jawo musu dimbin asara, musamman ma kananan manoma.
Kazalika, ya yi nuni da cewa; kamata ya yi a rika sayar musu da takin zamanin a kan lokaci, sannan kuma gwamnati ta sayar musu da shi cikin rahusa, wanda hakan zai ba su kwarin gwaiwar noma amfani mai yawa; wanda zai iya wadatar da wannan kasa.
Ita ma wata manomiya, Hajiya Aisha Abubakar a hirarta da wakilinmu ta bayyana cewa, matakin gwamnatin tarayyar ba zai wadatar wajen karya farashin abinci ba, domin kuwa Nijeriya na bukatar dimbin tantan na abinci; kafin a iya wadata kasar da abinci, musamman duba da karuwar yawan al’ummar kasar a halin yanzu.
Ta kara da cewa, rashin sama wa manoman ingantacce Irin noma, hakan na jawo musu tabka asara da kuma rashin mayar da hankali a bangaren gwamnati, musamman gwamnatin tarayya na samar da kayan aikin noma na zamani; wanda ko shakka babu ke yi wa fannin matukar illa tare da samar da koma baya.
Shi kuwa wani babban manomi, a bangare guda kuma tsohon shugaban kunkiyar masu kiwon kajin gidan gona, reshen Jihar Kaduna; Alhaji Musa Bala a zantawarsa da LEADERSHIP Hausa ya yi nuni da cewa, matakin gwamnatin tarayyar; tamkar riga Malam Masallaci ne, domin kuwa ko da an shigo da abincin, akwai wasu baragurbin da za su saye baki-daya; su kuma rika sayar wa da al’umma, musamman talakawa a kan farashi mai matukar tsada.
Bala ya kara da cewa, kamata ya yi yadda Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci a wannan fanni, sai kuma ya sa a dawo da tsari irin na da; wato na kafa hukumar kayyade farashin kayayyaki, musamman kayan abinci; amma wannan mataki na shigo da kayan abincin cikin wannan kasa, musamman domin magance hauhawar farashin kayan; ba zai taba yin wani tasiri ba.