Rashin ilimi tsakanin manya da matasa ya zama wata babbar matsala, wadda har ta sa masana suke ganin irin lamarin ne yake taimkawa wajen karuwar yaran da ba su zuwa makaranta a Nijeriya.
Ilimin manya ana gane shi ne ta kason mutane daga shekara 15 wadanda suke iya karatu da rubutu, tare da fahimtar ‘yar karamar magana a kan rayuwarsu ta yau da kullum.
Gwamnatin tarayya ta kiyasta lamarin wadanda ke da ilimi ya kai kaso 69, wannan ya nuna ke nan kaso 31 har yanzu su marasa ilimi, wanda kuma hakan yana nuna akwai mutane da yawa da basu da ilimi, wanda kuma hakan na nufin da akwai bukatar akwai abubuwan da suka kamata a yi ko daukar matakai dangane da hakan da zummar samun daidaiton da ake bukatar samu na wani mizani kamar fiye da kaso 90 na wadanda za su kasance masu ilimi.
- Gwamnatin Tarayya Ita Kadai Ba Za Ta Iya Daukar Dawainiyar Kudaden Ilimi Ba – Minista
- Gobara Ta Yi Sanadin Mutuwar Iyalan Kwamishinan Ilimi A Kano
Wadannan alkalumma da hukumar kula da kididdiga ta kasa ta fitar ya nuna sashen Arewacin Nijeriya shi ke da yawan al’ummar da basu da ilimi inda Jihar Yobe take mafi kankanta na kaso 7.23, Zamfara 19.16, Katsina na da kaso10.36 sai Sakkwato mai kaso 15.01, yayin da sashen Kudancin Nijeriya ke da yawan masu ilimi inda Jihar Imo ke jagorancin haka da kaso 96. 43, Legas kaso 96.3, Ekiti kaso 95.79,sai Ribas da take da kaso 95.76.
Wannan kididdigar ta nuna da akwai wagegen gibi tsakanin sassan biyu wanda ya nuna da akwai bukatar a dauki mataki domin a cike shi gibin da ke da shi, na maganin matsalar da ta sa ake samun yara wadanda basu zuwa makaranta a Nijeriya.
A kokarin ta na cike gibin ko gurbin da ake da shi hukumar kula da Ilimin manya da yaki da jahilci a wani taron da ta kir ana masuruwa da tsaki a Abuja, na yadda za a cimma buri na karuwar masu ilimin da ake bukata.
Da yake jawabi lokacin taron mai taken” matsalolin da ake fuskanta na gano yawan yaran da basu zuwa makaranta da matasa babban sakataren hukumar,Farfesa.Simon Akpama,’ya ce taron na wadanda za su taimaka sun hada kansu ne domin domin bunkasa ilimin yaki da jahilci a Nijeriya.
Ya kara bayanin cewa ba wata maganar boye- boye lamarin rashin ilimi a tsakanin manya da matasa wata hanya ce da matsalar yawan yaran da basu zuwa makaranta,ta biyo har ta samu wurin da zata boye.
“Bugu da kari ya kara bayani duk kokarin da ake na ganin an gano bakin zaren,akwai matsalolin da suke samar da karan- tsaye a kokarin da ake na kawo karshen rashin ilimi ko yaki da jahilcin manya da matasa,hakan ke taimakawa wajen karuwar yaran da basu zuwa makaranta.
Ya kara jaddada cewa ganin yadda lamarin yake ne yasa aka ga yafi dacewa inda har aka dauki mataki na maganin ko kawo karshen babbar matsalar da take damun kasa, inda aka dauki matakin ganin dukkan manya da matasa sun samu dama ta kasancewa masu ilimi bayan sun yaki jahilci.
Yayin da yake karin haske cewa ilimi bai tsaya kawa ikan iya karatu da rubutu ba,kamar yadda yace “ ilimi wani tubali ne inda ake fara gina gaba, domin yana ba kowa damar bunkasa al’umma da cigaban wajen samar da abubuwan more rayuwa”.
Babban sakataren yayin da yake bayani kan yadda za a fita daga matsalar kamar yadda yace lamarin yana hannun manya da matasa wadanda gabarasu ke da dama ta samar da ko kawo cigaba, “fatan da ake da ita da muradai ‘yan gida daya ne inda akwai hanyoyin karuwa masu dama in an samu yakar jahilci aka samu ilimi.”
Manufar wannan taron it ace kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su taimakawa kokarin da gwamnati take, inda iin aka hadza hannu daya za a iya gamawa da rashin ilimi ko jahilci, a sake saita ko daidaita tunanin manya da matasa su maida hankalinsu wajen bunkasa cigaban Nijeriya.
Akwai abubuwa da yawa wadanda suke taimakawa wajen karuwar jahilci a Nijeriya da suka hada da, jama’a kara yawa suke a Nijeriya, saboda karuwar da al’umma suke yi ne, shi yasa yawan wadanda basu yaki jahilci ba ke karuwa.