A baya-bayan nan ne taron tattaunawar duniya kan “Zurfafa gyare-gyaren kasar Sin a sabon zamani dama ce ga duniya” wanda rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG ya shirya, ya kaddamar da zama masu jigo na musamman kamar su gyare-gyare da kirkire-kirkire, da bunkasuwa mai inganci, da bude kofa ga kasashen wajen a babban mataki, da inganta yanayin zuba jari, gami da zama na musamman ga rukunonin kwararru kamar su cibiyoyin kasuwancin na kasa da kasa, masu sharhi kan harkokin kudi da masu sa ido. Taron ya gayyaci manyan baki daga kasashen ketare, da kwararrun Sinawa da na kasashen waje, da wakilan cibiyoyin kasuwanci na kasa da kasa, da shugabannin kamfanoni na kasa da kasa, da masu sharhi kan harkokin kudi, da sauran jama’a, da su yi magana game da kuzari da kwarin gwiwar da zurfafa yin gyare-gyare na kasar Sin ya kara a duniya, da yin tattaunawa game da dimbin damammaki da zamanantarwa irin ta kasar Sin ke kawo wa masu zuba jari na kasa da kasa da kamfanoni na kasa da kasa. (Mai fassara: Yahaya)