Ɗan wasan gaba na Manchester City Julian Alvarez, ka iya barin ƙungiyar a bana wanda hakan yasa Manchester City ta bayyana zunzurutun kuɗi har Yuro miliyan 77 a matsayin kuɗin da duk kungiyar da zai koma zata biya.
A cewar jaridar The Athletic, zakarun gasar Premier sun yiwa ɗan wasan Argentina kuɗi, wanda kuma a shirye suke su sayarwa duk mai buƙatar ɗan wasan gaban mai shekaru 22.
An tabbatar da cewar tsohon ɗan wasan na River Plate yana buƙatar ƙarin lokacin buga wasanni sannan kuma yana buƙatar ya samu waje mai dumamar yanayi ba kamar a Ingila da sanyi yayi yawa ba.
Atletico Madrid, wacce ta nuna sha’awar ɗan wasan, ba ta amince da buƙatar City ta biyan waɗannan kuɗaɗen ba kuma za ta iya ficewa daga duk wata yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan.