Kungiyar Fulani ta ‘Miyatti Allah Cattle Breeders Association of Niger (MACBAN)’ reshen jihar Katsina, ta nesanta kanta daga zanga-zangar da aka shiryawa gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu domin halin yunwa da wahala da ‘yan Nijeriya ke fama da shi.
Kungiyar ta ce wasu ne ke cusa wa matasan wannan ra’ayi su yi wa gwamnati bore, wanda ta ce zanga-zangar ka iya rikidewa ta koma tashin hankali.
Kungiyar ta bayyana hakan ne ta hannun Abdullahi Ismail, Sakatare na kungiyar reshen jihar Katsina a wata ganawa da ya yi da manema labarai.
Ismail ya ce; “na zo nan domin mu yi kira ga matasa wadanda za a yi amfani da su domin cimma manufa; akan suna korafi da yunwa da tsanani na rayuwa dake damun al’umma. Bayan kuma wasu ne ke cusa musu wannan ra’ayin. Wanda a zahirin gaskiya abin ba nan ya dosa ba. Shiyasa muke kiran al’umma musamman matasanmu da ka da a yi amfani da su wajen yi ma gwamnati barna ko wajen kawo wani rudani a cikin kasa”, ya shawarce su.
Sannan ya ci gaba da cewa; “matasan na duba da irin kasashen Kenya da sauran kasashe da suke irin wannan zanga-zanga. Mutanen wadancan wuraren suna yi ne domin kasar su da ci gabanta. Amma mu a fahimtarmu wannan zanga-zangar da za a yi ba zanga-zanga ba ce ta ci gaban al’ummar Nijeriya, wasu ne suka kirkire shi domin cimma manufofinsu”, in ji shi.
Kungiyar ta ci gaba da cewa; “a kan haka, shugaban kungiyar tabbatar da dimokuradiyya a Nijeriya, Honorabul Abdurrahman Buba Kwacham, ya tara wannan taro ya kira mutane masu ruwa da tsaki a kan shugabanci na matasa da abin da ya shafi arewacin Nijeriya da ma kasar baki daya a kan a gaya wa mutane muhimmancin rashin shiga cikin wannan zanga-zanga da za a yi”.
Kungiyar ta ce zanga-zangar ba na gaskiya bane, na cimma wadansu manufofi ne. “Ba ana yi bane domin wahalar da kasar ke ciki. Idan domin matsalolin da kasa ke ciki ne, akwai shirye-shirye da yawa da gwamnati ta yi, domin magance wadannan matsalolin”, ya labarta.
Ya nesanta kungiyar da cewa gwamnati ta siye su ne su kashe kwarin guiwar matasan, inda ya jaddada cewa; gwamnati ba ta siye su ba; sai dai ya yarda cewa akwai damuwa ta rayuwa da ‘yan Nijeriya ke fama da shi; “amma gwamnati na kan kokarin ganin ta magance wannan matsalolin. Hakan yasa muke ganin bai kamata matasa su sanya kansu a cikin wannan zanga-zanga ba”, ya lurantar.
Kungiyar ta ce ‘yancin gashin kai da aka bai wa kananan hukumomin Nijeriya, a ganin su tabbas zai magance matsaloli na tsaro sannan za a samu sauki; “domin ba sai sun jira gwamnatin jiha ko na tarayya ta kawo dauki ba. Domin suna da komai a hannunsu wanda za su yi amfani da shi domin magance matsalar tsaro domin taimaka ma al’umma”, in ji shi.
Da yake tabbatar da irin wahalar rayuwa da ‘yan Nijeriya ke fuskanta ya ce; tabbas akwai matsaloli wanda ya hassala ‘yan Nijeriya, amma akwai wadanda za su yi amfani da zanga-zangar wajen cimma manufofinsu, “akwai wadanda za su zo su bi masu yin abin don Allah, masu yi domin ci gaban kasar, su shiga cikinsu su rika balla shagunan mutane suna kawo rudani a cikin al’umma. Wanda daga karshe duk zai tafi da sunan wannan zanga-zangar da aka shirya a kan yunwa da tsananin rayuwa, bayan kuma a zahiri ba haka bane.
Ya karkare da cewa; “muna yin abu ne domin kyautata rayuwar matasa. Muna shugabantar matasa ne. Hakan ya sa mu ka ga ya kyautu mu kira matasan nan mu sanar da su cewa wannan abin da suke yi idan suka tafi da shi, akwai wadanda za su shigo bata gari su canza ma abin tsari da kuduri wanda suke kan shi”, in ji shi.