Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin sabon kwamitin gudanarwa na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars bayan ƙarewar wa’adin kwamitin da ya gabata.
Wannan matakin, wanda mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanar, an ɗauka ne don kawo kwararrun mutane masu ƙwarewa domin su yi wa’adin shekara guda, wanda za a iya sabunta wa bisa ga nasarar su. Sabbin mambobin da aka naɗa sun haɗa da Shugaba Ali Muhammad Umar (Nayara Mai Samba) da wasu mutane da za su kula da harkokin kungiyar.
- Katsina United Ta Kammala Ɗaukar Ƴan Wasa Biyu Daga Kano Pillars
- Katsina United Ta Kammala Ɗaukar Ƴan Wasa Biyu Daga Kano Pillars
An ɗorawa sabbin mambobin kwamitin nauyin yin aiki tare da Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Jiha da sauran masu ruwa da tsaki domin inganta ƙungiyar Kano Pillars FC. Gwamnan ya nuna ƙwarin gwiwa kan cewa ilimi da ƙwarewar mambobin kwamitin zai taimaka sosai wajen cimma burin ƙungiyar da kuma inganta aikinta a lokutan wasa masu zuwa.
Bugu da kari, Gwamna Yusuf ya naɗa Kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa, a matsayin Jakadan Wasanni na Jihar Kano. Shigar Musa cikin wannan aiki ana sa ran zai ƙarfafa gwuiwar ƴan wasa da kuma ƙara wa ƙungiyar daraja, wanda zai taimaka wajen bunƙasa ta da samun nasarar Kano Pillars FC.