Babu wani lokaci da ya fi dacewa da a dauki matakin kawo karshen yadda gine-gine ke rushewa a sassan kasar nan fiye da wannan lokacin. A ‘yan watannin nan an samu rushewar gine-gine da suka kai ga rasa rayukan al’umma da dama da kuma asarar dukiya na miliyoyin nairori, har lamarin ya kai ga zama abin kunya ga Nijeriya a idon duniya.
Kwanakin baya ne wata makaranta a yankin Busi Buji da ke karamar hukumar Jos ta arewa a Jihar Filato ta rushe inda akalla dalibai 22 suka mutu wasu 132 suka ji munanan raunuka.
- Matasa Sun Gudanar Da Zanga- zangar Lumana A Sakkwato
- Wang Yi Ya Jaddada Muhimmancin Diflomasiyya Tsakanin Mabanbantan Al’ummu
Yawancin wadanda suka mutu da wadanda suka tsira, dalibai ne matasa masu zana jarrabawar zangon karshe ta kammala matakin karatun sakandire lokacin da ginin ya ruso a kansu. Abubuwa da dama aka dora wa laifin rushewar ginin sun kuma hada da rashin amfani da ingantattun kayan aiki da kuma kasancewar ginin yana kusa da rafi, an kuma kwashe kwana uku ana tafka ruwa, abin da ya haifar da ambaliyar ruwa a yankin.
Bayanai sun nuna cewa, kusan shekara 18 (2006) da suka wuce hukuma ta ba masu ginin wa’adin su gaggauta rusa ginin saboda an fahimci ba su yi amfani da ingantattun kayan aiki da suka kamata ba, amma suka yi biris da gargadin hukumar suka ci gaba da aikin ginin har zuwa wannan lokacin da ginin ya rushe.
A nata tsokacin, hukumar kula da harkokin injiniyoyi ta kasa (COREN) ta sanar da cewa a tsakanin watan Janairu zuwa watan Yulin 2024 an samu rushewar gine-gine 22 a fadin kasar nan wanda ya kai ga mutuwar mutum 33.
A taron manema labarai da shugaban kungiyar ta COREN, Sadik Abubakar, ya jagoranta, ya bayyana cewa, a cikin rushewar gine-gine da aka samu a fadin kasar nan, Jihar Legas na da kashi 27.27 yayin da Abuja da Anambara ke da kashi 18.18 na rushewar gine-gine da aka samu.
Ya kumka kara da cewa, Jihar Ekiti da Filato ke da kashi 9.09 kowannesu yayin kuma da Jihar Kano, Taraba da Neja ke da kashi 4.55 na yawan gidajen da suka rushe a cikin wannan shekarar.
Kididdiga ta kuma nuna cewa, Jihar Legas ce a kan gaba na yawan gidajen da suka rushe inda aka samu gidaje 91 wanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutum 354 tun daga shekarar 2012.
Haka kuma bayani ya nuna cewa, an samu rushewar gidaje 30 a yankin Abuja wanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutum 63 wasu kuma da dama suka ji raunuka daban-daban tun daga shekarar 1993.
A ‘yan shekarun nan, rushewar gine-gine ta zama ruwan dare inda ta baya-bayan nan ita ce wanda ta faru a ranar 12 ga watan Yuni na wani a gida kusa da makarantar ‘Dennis Memorial Grammar School (DMGS)’ a garin Onitsha, ta Jihar Anambara bayan wadda ta faru a ranar 13 ga wagan Yuni a Jihar Filato da kuma wadda ta faru a uguwar Kubwa ta yankin Abuja ranar 14 ga watan Yuli.
Wannan jaridar ta nuna mamakinta a kan yadda duk da asarar rayuka da ake samu sakamakon rushewar gine-ginen har yanzu gwamnati ba ta nuna damuwarta ba, ballantana ta kaddamar da dokar tabaci a bangaren.
A ra’ayinmu, za a iya kauce wa wadannan rushewar gine-ginen idan har gwamnati ta mayar da hankali wajen sanya ido a kan masu gine-gine. Haka kuma da masu gine-ginen sun mayar da hankali wajen amfani da ingantattun kayan aiki da hakan bai kai ga faruwa ba.
Amma kuma wani abin lura shi ne duk rashin kula da aiki na wasu jami’an gwamnati da kuma babakeren ‘yan kwangila masu aiki, zuwa yanzu babu wanda aka kama tare da yanke wa hukunci a kan laifin rushewar gini. Duk da mace-macen da ake yi babu wanda aka kama.
Daga dukkan alamu masu hannu da shuni ba sa fuskantar hukuncin laifin da suka tafka sakamakon rushewar gini a Nijeriya. Za a iya tunawa da rushewar cocin ‘Synagogue Church For All Nations’ da kuma ginin nan mai hawa 21 da ke layin Gerard a Ikoyi dukkan su a Jihar Legas.
Bayanin da ake da shi a halin yanzu yana nuna cewa, babu wanda aka hukunta sakamakon rushewar gini a duk fadin Nijeriya.
Muna cike da mamaki na yadda har yanzu gwamnati da masu ruwa da tsaki suka kawar da kai daga daukar matakai a kan wannan abin da ke faruwa a kan idon kowa da kowa, ana kuma asarar rayukan daruruwan mutane sakamakon rashin kula da ka’idoji da dokokin gine-gine.
Muna kira ga gwamnnanti da ta tabbatar da hukunta duk wani mai gini da ya yi sakaci da dokokin gine-gine har aka samu rushewar gini domin haka ya zama darasi ga sauran al’umma, ta haka za rage irin asarar rayuka da dukiyoyin al’umma da ake yi a kullum.
Ya kuma kamata a tabbatar da hukunta duk wani jami’in gwamnati da ya yi wasa da aikinsa har aka samu gini ya rushe in har ba a hukunta jami’an gwamnati masu kula da ingancin gine-gine ba to da wuya a kawo karshen wannan matsalar, za a kuma ci gaba da samun matsalar rushewar gine-ginen kenan a sassan kasar nan.
A kan haka ne shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bukaci gwamnonin jihohi su karfafa dokoki a jihohinsu domin kawo karshen rasa raywukan al’umma da ake samu sakamakon rushewar gine-gine fadin kasar nan musamman abin da ya faru a Jihar Filato kwanakin baya.
A yayin da muke goyon bayan kiraye-kirayen shugaban Majalisar Dattawa na a kawo karshen rushewar gine-gine, muna kira ga masu ruwa da tsaki a bangaren gine-gine su kara kaimi wajen sa ido a kan gine-gine da ake yi domin tabbatar da suna bin dokokin da aka tsara tare da kuma tabbatar an hukunta duk wanda ya saba wa doka, ta haka za a kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Nijeriya.