Zanga-zangar yunwa da tsadar rayuwa da ta dauki hankulan al’ummar kasa tun daga makonni uku da suka gabata, ita ce irin ta ta farko da ‘yan Nijeriya suka fara aiwatarwa, tun bayan kafuwar wannan kasa; wanda hakan ya zama abin tattaunawar jama’a a ciki da wajen Nijeriya.
Dubun-dubatar jama’a, mabambantan kungiyoyin matasa da na dalibai da kungiyoyin fararen hula, sun shirya zanga-zangar ne daga 1 zuwa 10 ga Agustan 2024; sakamakon tsananin yunwar da ake fama da ita, wadda ke neman kassara al’umma.
- Munafurci Dodo Ne Me Shi Ya Kan Ci
- Wang Yi Ya Jaddada Muhimmancin Diflomasiyya Tsakanin Mabanbantan Al’ummu
Hakan ya biyo bayan cire tallafin man fetur, gurbacewar tattalin arziki, faduwar darajar naira, tashin gwauron zabon kaya, tabarbarewar tsaro da sauransu da suka sa aka kasa gane alkiblar da gwamnatin Tinubu ta dosa.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, dimbin jama’a na cike da zumudi, kagara da kuma dokin fara zanga- zangar a fatansu na samun canji da saukin rayuwa; bisa ga mummunan halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai da suke ciki, tun bayan kafuwar gwamnatin APC, wadda farashin kayayyaki ya nunnunka a karkashin jagorancinta, inda suke fatan gwamnati ta janye wasu daga cikin kudirorinta tsaurara.
A mabambantan ra’ayoyin jama’a, suna dokin gudanar da zanga-zangar ne; domin nuna wa gwamnati kuskurenta na assasa wasu kudire-kudirenta, wadanda suka jefa kasa da al’ummarta cikin kuncin rayuwar da ba a saba ji da gani ba; jim kadan bayan kamamala mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.
Haka zalika, akwai wasu da dama da ke fargabar gudanar da zanga-zangar; wadanda ke ganin za ta iya zama gagarumar matsala a fadin kasar. Masu irin wannan ra’ayi, na ganin wasu za su iya shiga cikin rigar zanga-zangar; su hargitsa kasa ta hanyar da tashin-tashinar da ba a san inda za ta kai ko za ta tsaya ba.
Gwamnatin Tarayya, wadda ita ce kan gaba wajen fargaba tare da zulumin zanga-zangar; ta yi duk mai yiyuwa don ganin ba a gudanar da ita ba, musamman ta hanyar kokarin yin amfani da jagororinta a jihohi, su dakatar da yi mata bore.
A kan wannan, gwamnati ta samu nasarar shawo kan kungiyoyin matasa da dama; wadanda suka fito fili suka sanar da duniya janyewarsu daga shiga wannan zanga-zanga. Kazalika, wasu matasan ma har fitowa suka yi, domin aiwatar da zanga- zangar kin goyon bayan wannan zanga- zanga, to sai dai kuma wasu kungiyoyi da matasa da dama; tamkar an kara musu kuzarin tunkarar zanga-zangar ne gadan-gadan tare da dokin zuwan ranar.
Domin shirin ko-ta-kwana kan wannan zanga-zanga, jami’an tsaro a fadin kasa bakidaya, sun dauki kwakkwaran shirin dakile duk wani kalubale da ka iya tasowa a yayin zanga-zangar ta lumanan; tamkar suna shirin tunkarar abokan gaba a fagen daga.
Matakin da ‘yansanda, sojoji da jami’an tsaron farin kaya na DSS suka dauka, ya haifar da korafe-korafe daga al’ummar kasa da suka bayyana cewa, idan har ana iya daukar gagarumin matakin shirin na ko-ta kwana- kan zanga- zangar da dokar kasa ta bai wa al’umma ‘yancin aiwatarwa, me ya hana a dauki matakin yaki da haramtattun ‘yan ta’addan da ke cin karensu ba babbaka da hana al’umma yin barci da ido daya.
Tun kasa da kwana daya da fara zanga-zangar, jami’an sojoji suka cika Birnin Tarayya, Abuja tare da mamaye manyan hanyoyin birnin; suka rika tsayar da ababen hawa suna binciken su. Haka nan ma, masu motoci da ke shiga Abuja; sun samu tsaiko na tsawon lokaci kafin yin bincike da kuma ba su damar wucewa. Mafi yawan ma’aikata da masu sana’oi a birnin, na zaune ne a garuruwan wajen birnin da garuruwan da ke kusa, wanda hakan ya tilasta wa wasu daga cikin su komawa gida bayan daukar awanni a shingen binciken.
Gwamnatin Tarayya, gwamnatocin jihohi da masu ruwa da tsaki; sun ci gaba da tursasa wa wadanda suka shirya zanga-zangar yunwa da tsadar rayuwa, domin zaunawa a teburin sulhu da gwamnati ta hanyar cewa, gurbatattu za su iya amfani da wannan dama, domin tayar da tashin-tashina; wadda suka ce ba a san irin illar da za ta haifar ba. A kan wannan, gwamnoni da dama sun bayyana haramcin zanga-zangar a jihohinsu; a daidai lokacin da jami’an tsaron farin kaya suka rika kama wadanda ke da hannu a zanga-zangar.
Kwana guda kafin zanga-zangar, Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun; ya bayar da umarni ga manyan jami’ansa da Kwamishoniinsa na jihohi 36 ciki har da Birnin Tarayya da su bayar da kariya ga masu zanga-zangar. Haka zalika, rundunar jami’an tsaron farin kaya (Cibil Defence), sun kebe jami’ai dubu 30, domin kare muhimman abubuwa daga lalacewa a yayin zanga-zangar.
Kazalika, Kwamishinan ‘Yansandan Birnin Tarayya, Abuja Bennett Igweh; ya umarci jami’ansa 4,200 da su tabbatar da kariyar masu zanga-zangar a Abuja tare da gargadin ka da a bayar da damar gudanar da kazamar zanga-zanga. Bugu da kari, a jihohi 36; jami’an tsaro sun tsaurara tsaro a ko’ina a cikin shirin ko-ta-kwana. A jihohin da dama tuni aka kafa shingayen biciken ababen hawa.
A makon nan ne dai, Mataimakin Shugaban Kasa; Kashim Shettima ya bayyana cewa, al’ummar kasa na da ‘yancin aiwatar da zanga-zangar, sai dai ana gudun gudanar da ita ce sakamakon irin illolin da za ta iya haifarwa.
A jawabin da Kakakinsa, Stanley Nkwocha ya fitar ya ce; idan aka ce za a gudanar da zanga-zangar, za a iya samun dimbin asara da dama, domin kamar yadda yake a tarihi wasu kan shiga cikin zanga-zangar da doka ta ba da dama; domin kawo tashin- tashina, wanda hakan kawai ake gujewa. Ya kara da cewa, Tinubu na da kyakkawar manufa ga al’ummar Nijeriya, don haka yana bukatar a bashi goyon baya da lokaci; domin cimma burinsa na raya wannan kasa.
A kokarinta na ganin ta dakatar da zanga-zangar, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa; babu bukatar gudanar da zanga-zangar, domin kuwa kusan gwamnati ta magance bukatun da masu zanga-zangar ke korafi; kamar yadda Minsitan ‘Yada Labarai, Muhammad Idris ya bayyana a matsayin sakamakon zaman majalisar zartarwa a karkashin jagorancin Shugaban Kasa a ranar Litinin da ta gabata.
Ya ci gaba da cewa, Tinubu ya yi kokarin rage radadin da jama’a ke ji, musamman ta fuskar rarraba abinci a jihohi, sayar da abincin a cikin rahusa da kuma kaddamar da bashin dalibai.
Haka nan, Minsitan ya bayyana cewa; wasu za su iya shiga cikin zanga-zangar don mayar da ita tashin hankali, don kauracewa hakan; mafita ita ce a zauna a samu fahimtar juna ba tare da an shiga wannan zanga-zanga ba. Ya ce, tuni gwamnati ta bayar da motocin abinci 20 ga kowace jiha; domin raba wa jama’a, kana akwai shinkafar da aka kai jihohi domin sayar wa da jama’a a kan rabin farashinta, wato Naira Dubu 40.
Bisa hasashen matsalolin da za su iya faruwa sanadiyar wannan zanga- zanga, gwamnatin tarayya ta bayyana gidajen gyaran hali; a matsayin wurare masu hadari, wanda ta ja hankali tare yin gargadin cewa; bai kamata a yi wasa da su a kowane irin yanayi ba.
Shugaban hukumar, Halliru Nababa ne ya bayyana hakan tare da nuni da cewa, duk wani ko wasu gungun mutane da ba su da alaka da gidan, wajibi ne su kaurace masa. Ya ce, gidan gyaran hali; wani muhimmin waje na kasa, wanda duk wani yunkuri na kai masa farmaki zai haifar da karya doka da oda; don haka ya zama dole a kiyaye. Sannan, hukumar ta bukaci jama’a su bayar da hadin kai tare da goyon baya, don kare gidajen. Kazalika, ya kuma bayyana cewa, sun tanadi jami’an tsaro; domin ganin ba a taba ko guda daga cikin wadannan gidaje na gyaran hali ba.
A nata bangaren kungiyar gamayyar shugabannin jam’iyyar APC na jihohi 36 ciki har da Abuja, sun bayyana zanga-zangar a matsayin wani yunkuri na kawar da gwamnatin Tinubu; wanda hakan ya sa suka sanar da fara taron jaddada goyon bayansu ga gwamnatin.
A yayin da ake kwana guda kafin fara shiryayyiyar zanga- zangar, shugabannin shiyoyin Arewa da Kudu; sun bi bayan wadanda suka nesanta kansu da gangamin taka wa gwamnati burkin tsare-tsarenta marasa alfanu. Dalilin rashin goyon bayan nasu kuwa shi ne, kan cewa akwai yiwuwar zanga-zangar lumanan za ta iya komawa tashin hankali ko kuma wani makamancin haka.
Fitacciyar kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), wadda ita ma ta nesanta kanta da wannan zanga-zanga, ta yi gargadin cewa za ta iya zama silar asarar rayuka da dukiyoyi tare kuma da mayar da ci gaban da aka samu a Arewa baya duk kuwa da cewa, babu daya daga cikin dalilin yin zanga-zangar; musamman idan aka yi la’akari da matsalar tsaro da ya kassara yankin Arewa tare kuma da haifar da matsalar karancin abinci.
Kakakin kungiyar, Farfesa Tanko Muhammad Baba ya bayyana cewa; akwai mamaki matuka yadda miloyoyin ‘yan Nijeriya, wadanda ba su da abincin da za su ci a kullum; ke kokarin gudanar da zanga-zangar tsawon kwanaki 10, wanda kuma ba a san wadanda suka assasata ba.
A nata bangaren, gamayyar kungiyar shugabannin jam’iyyar APC a jihohi 36, ta bayyana rashin dacewa tare da nesanta kanta da goyon bayan wannan zanga-zanga. Sakataren kungiyar, wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kuros Riba, Alphonsus Eba ne ya bayyana hakan, a taron manema labarai a Abuja tare da yaba wa ‘yan Nijeriya kan hakurin da suka yi na tsawon shekara guda. A daya bangaren kuma; sarakuna da shugabannin addini sun roki a bai wa Tinubu lokaci ya aiwatar da kudire-kudirensa na canji.
Haka nan, su ma sauran shugabanni da masu ruwa da tsaki a jihohi tara na Yankin Neja-Delta, sun nesanta kansu da sauran jama’arsu daga shiga wannan zanga-zanga. Sun cimma wannan matsaya ne a garin Fatakwal wajen taron al’ummar yankin, wanda Hukumar Bunkasa Yankin Neja-delta (NDDC) ta shirya.
A jawabinsa a wajen taron, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Goodwill Akpabio ya bayyana cewa; al’ummar yankin sun dauki matakin kaurace wa zanga-zangar ne, domin kuwa babu daya daga cikin bukatun masu zanga-zangar da yake da alfanu ga al’ummar yankin.
Ya kara da cewa, a baya yankin na fama da matsaloli iri daban-daban; amma Shugaba ‘Yar’Adua ya share masu hawaye, don haka a yanzu suna zaune lafiya duk da cewa; suna da matsalolin hanyoyi wadanda ba sa cikin bukatun da masu zanga-zangar suka gabatar.
Tuni dai jagororin zanga-zangar suka ki amincewa da bukatar Sufeto Janar na ‘Yansanda, Kayode Egbetokun; wanda ya bukaci su gudanar da zanga-zangar a kebantattun wurare, maimakon gangamin zagaye tituna.
A cewarsa, ba daidai ba ne a rika zagaye tituna a yayin zanga-zanga, wanda ya ce; a yayin da suke zanga-zangar tuni wasu sun shirya tayar da hankali, don haka ya bayar da shawarar canza tunani; domin ka da abin da ba a zata ba ya faru.
A kan wannan, babban lauyan kasa; Ebun- Olu Adegboruwa, wanda kuma shi ne lauyan kungiyar ‘Take it Back Mobement’, daya da cikin kungiyoyin da suka shirya zanga-zangar ya bayyana cewa; ko kadan ba su aminta da bukatar ‘Yansandan ba. Ya ce, za su gudanar da zanga-zangarsu ta lumana a saman tituna tare da kiyaye dokar da ta ba su ‘yancin aiwatar da zanga- zangar.