A ranar Alhamis 25 ga Yuli, 2024, aka gudanar da wani taron kara wa juna sani a Cibiyar Al’adun Kasar Sin da ke Babban Birnin Tarayya Abuja mai taken “Gyare-gyaren kasar Sin a Sabon Zamani”.
Taron wanda aka gudanar bisa hadin gwiwar cibiyar al’adun da Hukumar Kafofin Watsa Labarai ta Kasar Sin (CMG) ta samu halartar kwararru da manyan baki wadanda suka yi karin haske a kan gyare-gyaren da kasar Sin ta tsunduma yi da kuma alfanunsu ga al’ummar duniya.
- Majalisar Dattawa Ta Bukaci NEMA Ta Kai Wa Manoman Citta Dauki A Kaduna
- Sin Ta Damu Kisan Shugaban Hamas Zai Iya Haifar Da Babban Tashin Hankali A Gabas Ta Tsakiya
An fara taron ne da gabatar da jawabin Mataimakin Daraktan Sashen Yada Labarai na Kwamitin Tsakiya na Jam’iyyar CPC kuma Darakta Janar na Hukumar Kafofin Watsa Labarai ta Kasar Sin, Mista Shen, inda ya nuna muhimmancin dorewar hadin gwiwa tare da mika godiya ga mahalarta taron.
Mista Shen, ya jaddada wajibcin hadin kai a tsakanin al’ummomin duniya domin cimma muradun ci gaba da kowa da kowa ke hankoron gani.
Har ila yau, masu gabatar da jawabai daban-daban a wurin taron sun yi gamsassun bayanai game da rawar da kasar Sin ke takawa wajen taimaka wa ci gaban kasashen duniya.
Musamman wacce ta yi fashin baki a kan tasirin da kasar Sin ke yi wajen bunkasa tattalin arzikin duniya, Fa’iza Muhammed, ta ce ba karamar gudunmawa kasar Sin ta bayar wajen daidaita turbar habakar tattalin arzikin Nijeriya ba.
A nata bangaren, wakiliyar Ministar Bunkasa Yawon Bude, Misis Patricia Naria, ta mayar da hankali ne a kan yadda za a ciyar da harkokin yawon bude ido gaba a Nijeriya, kana ta nemi a karfafa matasa domin takaita kwararar mutane daga kauyuka zuwa birane.
Shi kuwa, Mista Raphael Oni, ya yi bayani ne a kan abubuwan da za a iya cimmawa idan aka samu hadin gwiwa da inganta kwazon aiki tsakanin kasashen duniya, kana ya yi tsokaci a kan irin rawar da Sin ke takawa wajen samar da ma’aikata a sassa daban-daban na ci gaban Nijeriya.
Shugaban Kungiyar ‘Yan Nijeriya Da Suka Samu Horo a Kasar Sin, Malam Mohammed Sulaiman, ya yi karin haske a kan muradun ci gaban kasa da Sin ta sanya a gaba da kuma kokarin da take yi na zamanantar da harkokinta tare da tabbatar da dorewar bunkasar duniya da zurfafa ci gaban kimiyya.
Ya kuma bayyana cewa, ga masu lura da matakin ci gaban kasar Sin, za su fahimci yadda kasar ta dage wajen fafutukar ganin su ne kan gaba a tsakanin sauran kasashen duniya, a bangaren tattalin arzikin kasa, domin samar da wadata a yankunansu.
Zauran majalisa ta uku, ya bai wa China damammaki iri daban-daban, wadanda suka hada da kamfanoni mallakar gwamnati da kuma sha’awar fuskantar babban kalubale na dunkulewar duniya wuri daya, in ji shi.
Sulaiman ya ci gaba da cewa, taron bana kan sauye-sauyen tattalin arziki da zamantakewa a kasar Sin, mai yiwuwa nan da shekarar 2029 a sake nazari a kan sabbin kalubalen da ke tunkarar duniya baki-daya.
Haka zalika, kasar Sin ta mayar da hankali wajen kyautata masana’antu gwamnati a matsayin na sahun gaba tare kuma da kyautata harkin bin doka da oda a fadin kasar baki-daya.
Daga bangaren Mista Okon Emmanuel kuwa, ya nuna muhimmancin shigar da matasa ne cikin harkokin yawon bude ido domin a dama da su, yayin da ita kuma Edi-ima Ekpety ta yi bayyana abubuwa masu ban sha’awa da ta koya a kasar Sin lokacin da take karatu a can inda ta nuna alfanun sanin al’adun juna da kuma damammakin karo ilimi da ake samu.
Ekpety Edi-ima; ta bayyana abubuwan da ta koya da kuma irin abubuwan da ci karo da su na ban sha’awa a fadin kasar.
Edi-ima ta ce, ta ziyarci kasa Sin ne kwanan nan; domin halartar taron taron kara wa juna sani, wanda ya kunshi mutum 18 daga kasashe bakwai na yankin kudu maso kudu.
Haka zalika, an shirya taron kara wa juna sanin ne; don sake karfafa alakar kasar Sin da kuma kasashen nahiyar kudu maso kudu da ke yankin Afirka. Babu shakka, wannan ziraya a cewarta, ta ba damar sanin wani bangare na rayuwar Sinawa da kuma irin ci gaban da suka samu.
Ta kara dacewa, abu na farko da ya fara burg eta shi ne, ganin yadda aka shuka filawa a kan hanyoyinsu, wanda ya sake kawata kasar yadda ya kamata. “Duk titinan da ka bi, haka za ka samu wadannan filawowi masu matukar ban sha’awa da kuma burgewa,” in ji ta.
Hakanan, a bangaren abin da ya shafi harkokin sufuri, mun koyi yadda za mu yi amfani da jirgin kasa da hawa motoci.
An dai kammala taron ne da jawabin mai gabatar da taron wanda ya nuna muhimmancin abubuwan da baki masu gabatar da jawabai suka bayyana tare da daukar hotuna da ke nuna sabunta hadin kai da zumunci a tsakanin mahalarta taron.
Za a iya cewa taron na kara wa juna sani da aka gabatar, ya samar da wata kafa ta tattaunawa da musanyar ra’ayoyi da kuma Karin haske a kan manufar gyare-gyaren da Sin ke yi da yadda abin zai amfanar da duniya tare da jaddada muhimmancin hadin gwiwa a tsakanin Nijeriya da Sin domin a gudu tare a tsira tare.