Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai. Assalamu alaikum.
Addinin Musulunci ya tabbatar, kuma zamantakewa da halin rayuwa ta yau da kullum, duka sun tabbatar a ilmance, cewa, halin kunci, da halin matsin rayuwa, da talauci, da yunwa, da fatara, tabbas suna da mummunan tasiri da hadarin gaske a cikin addinin al’umma. Suna kuma ruguza zaman lafiyar dan Adam da tunaninsa baki kaya. Ta yadda za ka ga matasan mu suna afka wa cikin halin shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran kayan maye. Sannan kuma laifuka irinsu zinace-zinace, kisan kai da zubar da jini, sace-sace, ta’addanci, hargitsi, hayaniya, rashin zaman lafiya da sauran ayukkan ashsha, su kan karu a cikin duk wata al’umma, wadda halin talauci da halin matsin rayuwa suka yiwa katutu.
Tabbas, Malaman addini suna ta kokari, ba dare ba rana,wurin karantar da al’umma da wa’azuzzuka da hudubobi da wayar da kan jama’a, tare da dora su akan tafarki madaidaici, Allah ya saka masu da mafificin alkhairi duniya da lahira, amin.To amma mu fada wa kawunan mu gaskiya komai dacin ta, ba tare da jin tsoron zagi ko zargin wani mai zargi ba, cewa, wallahi duk karantarwa da wa’azi da malamai zasu yi, matukar ba’a dakatar da halin matsin rayuwar da al’umma suke ciki ba. Matukar ba’a fito da hanyoyi ingantattu, da za’a magance ko a rage radadin wannan bakin talauci da ya addabi al’ummah ba. Matukar ba’a fito da tsare-tsare na gaskiya,na tsakani da Allah, na imani da tausayi da tsoron Allah ba, to al’umma ba zasu saurari kowa ba. Wannan shine gaskiyar maganar,kuma mutane basu son muna fadar hakan, saboda basu san irin abubuwan da muke ji kuma muke gani suna faruwa a cikin al’umma ba!
Wallahi na hadu da matar da nayi ma wa’azi da cewa taji tsoron Allah, ta daina yawon banzar da take yi, wallahi ta ce dani, Malam ba da so na nake yin wannan yawon ba. Abubuwa ire-iren wadannan, suna nan da yawa, ba sai na fito duk nayi ta bayyana su daya bayan daya ba.Duk wanda ya sani ya sani, wanda kuma bai sani ba, bai sani ba.
Don haka ne kullun Manzon Allah (SAW) yake neman tsari sosai daga talauci, har yake hada shi da kafirci wurin addu’arsa, domin sanin cewa, talauci aboki ne ga kafirci, kuma yana iya sa mutanen kirki su zama mutanen banza, kirikiri suna gani ba yadda zasu yi.
Hakika, babu wanda ya san talauci sai wanda talauci ya kama! Da mutum zai wuni tun daga safe har zuwa dare bai ci ba, shi da iyalansa, da zai gane me ake nufi da babu, kuma da zai san mene ne talauci!
Wallahi, wallahi, wallahi, Allah shine shaida, kuma zan mutu in tashi a gaban Allah, ranar Laraba 24/07/2024, da idona, na ga mutum uku, sun zo wurina a kan kwanansu daya ba su ci abinci ba, su da iyalansu. Mutum biyu kuwa, su kuma kwana biyu babu abin da suke ci sai ruwa kawai! Kai irin wadannan misalan suna nan da yawa, mu da muke cikin al’umma, kuma ake damun mu kullun, mu muka san matsalolin. Don haka babu bukatar ma kayi ta fadar wannan, domin Allah da ake yi domin sa ya sani.
Irin yanayin halin da al’umma suke ciki a kasar nan, na kunci da talauci da matsin rayuwa,don Allah ina ma suka ga natsuwa da hankalin sauraron wa’azin ka, ina suka ga dama da natsuwar tsayawa suyi Ibada, ko su bautawa Allah yadda ya kamata? Ya kamata mu gane hakan!
Ina yi maku rantsuwa da Allah, ba tare da kuna bi na bashin rantsuwa ba, duk wani aikin laifi da fasikanci da ta’addanci, kai da duk wata irin badalar da ka sani, yau a kasar mu Najeriya sun karu, duk sanadiyyar halin kunci da talauci da matsin rayuwa da al’umma suke ciki.
Kuma wallahi babu yadda zaka iya hana mutane aikata wadannan, ba tare da kai kabi hanyar da ta dace wurin basu gudummawa da wayar masu da kai, yadda ya kamata, domin Allah ya taimaka su daina ba.
Ni fa shi yasa nike samun matsala da wasu mutane wadanda basu fahimce ni ba. Ba zan yaudare ka ba, don haka kai ma kar ka yaudare ni, domin yaudarar juna babu kyau.Mu tsaya tsakaninmu da Allah, mu bi hanyar da ta dace, kuma hanyar gaskiya, domin kawo karshen matsalolin mu.
Ko shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da yake shugaban kasar Nijeriya ne, wallahi ni ban yarda yafi ni son Nijeriya ko kishin Nijeriya ba, to bare wani dan-kuci-ku-bamu.
Duk abinda ka sani mai matukar muhimmanci a gare ka, kai hatta rayuwa,wallahi ina iya sadaukar da ita, domin kishin addinina, da kasa ta da al’umma ta.
Don haka gaskiyar magana ita ce, addini ma da Ibada da duk wata bautar Allah da aka sani, ba zasu taba yiwuwa ba, cikin kwanciyar hankali da natsuwa, matukar mutane suna cikin irin wannan hali na kunci da talauci da matsin rayuwa da suka samu kansu a ciki ba tare da sun shirya masu ba.
Allah ya halicci bayinsa ne ba don komai ba, sai domin su bauta masa, shi kadai, ba tare da sun hada shi da kowa ba a wurin bautar ba; suyi da’a da biyayya ga fiyayyen halitta (SAW), kamar yadda ya fada a cikin Alkur’ani. Allah ya wajabta wa bayinsa, su tsayar da tauhidi, su guji shirka, su guji bidi’o’i, su guji saba masa, su guji dukkanin wani aikin barna da aikin badala da aikin ta’addanci a cikin al’umma. To amma idan aka kakabawa bayin Allah wata damuwa da zata hana su yin abinda Allah ya umurce su, suka je suna yin ba daidai ba, ba da son ransu ba, to mu sani, duk alhakin hakan yana kan duk wadanda suka jefa su cikin halin da suka samu kansu a ciki, har suka bijirewa Allah mahaliccinsu!
Muyi wa kawunan mu adalci, wallahi kowa yasan kasar mu Nijeriya ba haka take ba a baya. Yanzu ne da muka samu kawunan mu cikin matsalolin siyasa da shugabanci, aka wayi gari ayukkan ashsha suka yi mana katutu, har suke neman kawo tarnaki ga zaman lafiyar kasar.
Talauci da kafirci ’yan uwan juna ne, tare suke tafiya,daya ba ya rayuwa sai da daya! Kuma yunwa ita ce ma’aunin talauci na farko.
Wallahi a cikin wannan al’umma, saboda halin yunwa, talauci da matsin rayuwa, akwai masu tunanin cewa su ko sun yi Sallah ma ba za’a karba ba, don haka bari ma su bar sallar.
Ni a garin Okene na jihar Kogi na ke zaune, anan nake rayuwata. Koda yake ina rayuwa ne tsakanin Gusau da Okene. Amma wallahi irin famar da muke yi da ‘yan uwan mu Musulmi, musamman ma mata, anan garin Okene, na yawan riddar da suke yi suna barin addinin Musulunci, abin ba kadan bane. ‘Yan uwan mu mata suna yawaita yin ridda su fice daga Musulunci. Kuma wallahi mafi yawa, halin yunwa da kunci da matsin rayuwa yake sa suna yin wannan.
Allah shine shaida, muna iyakar kokarin mu gwargwadon karfin mu wurin dakatar da wannan barna, amma a gaskiya, abokan zaman mu kiristoci, suna neman sufi mu karfinmu. Kuma ba wani abu yake Jan hankalin mata Musulmi wurin yin ridda ba, illa irin gudummawar da suke samu daga wurin kiristoci.
Dani da dalibai na, da duk wanda Allah ya kaddari ya taimaka, mune kadai muke yin wannan aiki.Duk wata irin gudummawa da muke nema wurin ‘yan uwan mu Musulmi, ba samu muke yi ba. Kai wasu ma gani suke yi, cin kudin su zamu yi shi yasa basa taimakawa.
Idan mun nemi masu dukiya su taimaka a cikin ayukkan mu, basu taimakawa. Sun mayar da mu matsiyata. Babu wanda yake sauraronmu.Babu ruwan kowa da ra’ayinmu.Ana kallonmu a matsayin wadanda suka gaza a rayuwa, wadanda basu zo duniya da sa’a ba, wadanda ba su da wayo, wawaye, kuma jahilai. Kawai duk wannan,saboda mun ki bin hanyoyin shirmen da ake yi.Kowa wai ba zai taimake ku ba sai kun bi ra’ayinsa, ko muyi abinda yake so.Mu kuma da ikon Allah, mun yarda mu rayu a cikin halin rashi, da mu sa kan mu cikin ka-muya-muya!
Ba zaka ga talauci a bayyane ba, sai ka shiga garuruwanmu, sai ka shiga kauyukan mu da karkarar mu. Inda babu abinda kowa yake yi, illa kawai neman abin da zai ci, musamman lokacin bazara.Mabukata da mabarata da masu neman a agaza masu sun yi yawa kuma sun karu a cikin al’ummar mu.Wadansu ma saboda halin rashin tsaro da halin kunci da matsin rayuwa, ya kan sa suyi kaura daga kauye su tare a birane.
Yau a cikin al’ummar mu, mutane nawa ne suke iya biyan kudin wutar lantarki? Ko kudin makaranta, ko na asibiti ko kudin haya, ba tare da sun nemi taimako ko tallafi daga ‘yan uwa ko kungiyoyin taimakon marayu da gajiyayyu ba?
Ni a gani na, maimakon gwamnati tayi ta bayar da tallafin shinkafa, tallafin ma da sam baya isa hannun talakawa, ya kamata ta fito da tsarin bayar da jari domin al’umma su kafa kansu, a taimaka masu a gwamnatance. Ta yadda matasa zasu tsayu da kafafuwansu. Amma maimakon ayi wannan, sai aka wayi gari a halin yanzu ba wadanda ake cuta sai matasa ’ya’yan talakawa an bar su a wulakance, sai an zo zabe a nemo su, da an ci zabe kuma ayi watsi da su.
Lalle Gwamnatoci su farfado da tsarin raya karkara, ta yadda duk abin da zaka nema a birni akwai shi a kanannan hukumomi. Amma a yau ko jarida, banki, man salak, kake nema sai ka shigo birni.
Gwamnati ta kai kamfanoni kauyuka, inda za a kafa kananan masana’antu.
Kuma gwamnati ta sa ido sosai, domin a kore dabi’ar nan ta yin kudi dare-daya, ta hanyar kyautata wa wadanda suka yi abin kirki.Ta yadda Sarkin gari zai gayyace su, ya yaba masu, a basu sarautu tare da karrama su, a bayyana kwazonsu.Sabanin yadda muke gani a yau, ana ta karrama mabarnata, wadanda ba’a san asalin dukiyoyinsu ba, wadanda ba su taimakon al’umma.
Yin haka yana daga cikin hanyoyin yaki da cin hanci da rashawa.Kada a tsaya ana kama barayin awaki da barayin kaji, bayan ga manyan barayi nan suna shakar iskar ’yanci, wadanda suke kassara al’umma.
Wallahi idan aka tsayar da adalci a cikin al’umma, idan aka taimaki ‘yan kasa, idan mutane suka samu kulawa ta musamman, idan ma’aikata suka samu karin albashi, idan mawadata suna bayar da sadaka da zakka, zuwa ga wadanda suka fi cancanta, to hakan zai toshe duk wata kafa ta kwadayi da zari da handama da babakere, kuma wannan zai rage talauci, yunwa da halin kunci da matsin rayuwar da ake ciki.