• English
  • Business News
Wednesday, November 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jami’an Tsaro Sun Yi Harbi Kan Ƴan Jarida Da Masu Zanga-zanga A Abuja

by Abubakar Sulaiman
1 year ago
Zanga-zanga

Jami’an tsaro a filin wasa na Moshood Abiola National Stadium da ke Abuja sun buɗe wuta kan masu zanga-zanga da Ƴan Jarida a rana ta uku na zanga-zanga kan yunwa da ƙuncin rayuwa.

Zanga-zangar, wadda ta fara cikin lumana, ta canza yanayi a ranar Asabar yayin da Ƴansanda suka harba hayaƙi mai sa hawaye da harsasai cikin iska, suna tarwatsa masu zanga-zangar da suka fara sake taruwa.

  • Sin Ta Fadada Manufar Yada Zango A Kasar Ba Tare Da Biza Ba Zuwa Karin Tashoshi
  • Rana Ta 3: Duk Da Dokar Hana Fita Masu Zanga-zanga Sun Fito A Kano

Jami’ai masu rufe fuska daga hukumar tsaro ta DSS sun iso wurin kuma nan take suka shiga cikin martani, wanda ya haifar da kamawa da kuma jikkatar mutane da dama.

Wannan ruguntsumin  ya rutsa har zuwa ga Ƴan Jarida, inda harsasai suka samu motar da ke ɗauke da su yayin da suke ƙoƙarin barin wurin. Cibiyar kula da Ƴan Jarida ta Duniya (IPC) ta yi Allah wadai da waɗannan hare-hare, tana nuna damuwa kan yawaitar cin zarafi, da duka da hana Ƴan Jarida damar yin aikinsu a jihohi daban-daban.

Ƴan Jarida a Lagos, da Kano, da Abuja, da Calabar, da jihar Delta sun ruwaito cewa an ci zarafinsu, an ji musu rauni, kuma an lalata kayayyakin su daga hannun Ƴansanda da Ƴan daba.

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

‘Yansanda Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Kwara

Melody Akinjiyan, jami’ar kare ƴancin Ƴan Jarida ta IPC, ta soki waɗannan ayyuka, tana bayyana su a matsayin “wani abin alhini da ke maimaituwa a tarihi” kuma ta jaddada muhimmancin ƴancin Ƴan Jarida na rawaito al’amuran al’umma. Ta yi kira ga hukumomin tsaro da su binciki waɗannan hare-hare kuma su tabbatar da adalci ga Ƴan Jaridar da aka cutar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma
Labarai

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

November 4, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi
Labarai

‘Yansanda Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Kwara

November 4, 2025
tinubu
Labarai

Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU

November 4, 2025
Next Post
Me Ya Sa Budurwa Take Juya Wa Saurayi Baya Farad Daya?

Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

November 4, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Kwara

November 4, 2025
‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba

‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba

November 4, 2025
tinubu

Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU

November 4, 2025
Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar

Sin Na Goyon Bayan Najeriya Wajen Jagorantar Al’ummarta Zuwa Hawa Turbar Neman Ci Gaba Daidai Da Yanayin Kasar

November 4, 2025
2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC

2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC

November 4, 2025
Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

Li Qiang Ya Zanta Da Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

November 4, 2025
Karancin Abinci: Kofar Ofishin Tinubu A Rufe Take, Har Wasu Ministoci Ba Su Iya Ganinsa – Ndume 

Zargin Kisan Kiyashi Ga Kiristoci: Trump Bai San Ƙalubalen Tsaron Da Najeriya Ke Ciki Ba — Ndume

November 4, 2025
Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

Tsohon Jami’in Diflomasiyyar Nijar: Baje Kolin CIIE Muhimmin Dandali Ne Na Bunkasa Hadin Gwiwa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

November 4, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.