Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa, an dawo da tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta cire a shekarar 2023 sakamakon hauhawar farashin kayayyaki.
Shugaba Bola Tinubu a jawabinsa na farko a ranar 29 ga Mayu, 2023, ya bayyana cewa, tallafin man fetur ya tafi.
- Masu Shigo Da Mai Za Su Kawowa Matatar Dangote Cikas – Obasanjo
- Ba Don Tonon Gwal Na Ke Gina Gadoji Ba – Gwamnan Bauchi
Wannan kalaman ya haifar da tashin farashin man fetur daga kimanin naira 200 zuwa fiye da naira 600 kan kowace lita.
A wata hira da jaridar Financial Times, Obasanjo ya caccaki yadda gwamnati ta cire tallafin ba tare da la’akari da abun da zai haifar ba.
A cewarsa, kamata ya yi gwamnati ta aiwatar da wasu matakai kafin cire tallafin.
Amma tsohon shugaban ya bayyana cewa, tallafin ya “dawo” saboda yawan hauhawar farashin kayayyaki.
“Akwai ayyuka da yawa da ya kamata a yi. Ba wai kawai ka tashi da safe ka ce ka cire tallafin ba. Saboda hauhawar farashin kayayyaki, tallafin da aka cire bai tafi ba. Ya dawo,” in ji Obasanjo.