Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa (NHRC) ta yi Allah-wadai da kisan wani matashi dan shekara 16 mai suna Isma’il Muhammad da wani soja ya yi a lokacin dokar hana fita ta sa’o’i 24 da aka sanya don dakile zanga-zangar adawa da kuncin rayuwa a Zariya, Jihar Kaduna.
Sakataren zartarwa na Hukumar Dr. Tony Ojukwu, SAN a lokacin da yake mayar da martani kan lamarin, ya ce, abin takaici ne musamman ganin yadda Hukumar a baya ta yi gargadi kan wuce gona da iri kan masu zanga-zanga.
- Jami’an Tsaro Sun Yi Wa Ofishin NLC Dirar Mikiya Don Neman Hujja Kan Zanga-zangar Yunwa
- Ya Kamata Gwamnatin Tarayya Ta Kawo Karshen Matsin Rayuwa – Gwamnan Bauchi
Ojukwu ya sake nanata cewa, dole ne a kare ‘yancin dan Adam kuma ba zai yi wu a tauye shi ba a kowane hali, ya kuma kara da cewa, amfani da muggan makamai a kan fararen hular da ba su da makami, musamman kananan yara, abu ne da ba za a amince da shi ba, kuma ya saba wa ka’idojin kare hakkin bil’adama na duniya.
“Muna bukatar a gudanar da cikakken bincike a kan lamarin tare da yin kira da a hukunta sojan da ya aikata wannan mummunan abun,” in ji shi
ya kuma kara da cewa, “Hukumar NHRC za ta ci gaba da sanya ido kan lamarin tare da daukar matakan da suka dace don tabbatar da cewa an kare haƙƙin ɗan adam a Nijeriya.