Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kebbi, KESIEC, ta musanta zargin alaka da jam’iyyar APC da nuna son kai a zaɓen ƙananan hukumomin da jam’iyyar PDP ta yi a jihar.
A wata ganawa da manema labarai, shugaban hukumar da mambobin sun tabbatar da cewa shugabancin ba ya nuna son kai ko alaka da ‘yan jam’iyyar APC. Sun kuma musanta ikirarin gabatar da kuɗaɗen gudanarwa ga ‘yan takara da jam’iyyu, da kuma canjin da aka samu kwatsam na wa’adin biyan wadannan kudade.
- Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Kasuwar Dodoru A Jihar Kebbi, Rumfuna Da Yawa Sun Lalace
- Jam’iyyar PDP Ta Janye Daga Shiga Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kebbi
Ya kara da cewa, “muna da umarnin kotu da ya yarda da cewa kuɗaɗen gudanarwa na ‘yan takara da jam’iyyu bai saɓawa ƙa’ida ba”, in ji Kaura Dan-Hakimi.
PDP Ta Shafta Karya, Ba Mu Da Wata Alaƙa Da APC –
KESIEC ta jaddada ƙudirinta na gudanar da sahihin zabe na gaskiya da adalci, inda ta bada misali da yadda ya gudanar da zabukan marasa son rai tun farkon kafata har zuwa yanzu.
Kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa, Alhaji Muhammad Kaura Dan-Hakimi, ya sake nanata matakin da hukumar ta ɗauka na tabbatar da gaskiya da adalci, ya kuma yi kira ga bangarorin da kada su firgita ga zaɓen da za a gudanar a ƙarshen watan nan da muke ciki.