Rundunar ‘Yansandan jihar Kano ta kama mutane 873 bisa zargin aikata laifukan fashi da makami, da garkuwa da mutane, da kuma sauran laifuka yayin zanga-zangar da ta gudana. An kama waɗannan mutanan ne a faɗin jihar, kuma an gabatar da su a Shalƙwatar rundunar da ke Kano a yau Litinin.
Kwamishinan ‘Yansanda, Salman Dogo, ya bayyana cewa an kama mutune 600 bisa zargin aikata laifuka daban-daban yayin zanga-zangar a sassa daban-daban na jihar. Bugu da ƙari, an kama mutum 150 saboda karya dokar hana fita, sannan kuma mutum shida an kama su bisa laifin lalata da fasa shaguna a kamfanin Buga takardu na jihar Kano.
- Direba Ya Bai Wa ‘Yansanda Jakar Maƙudan Kuɗi Da Ya Tsinta A Kano
- Hukumar Kashe Gobara Ta Kano Ta Ceto Mutum 154 Da Kadarorin Naira Miliyan 80 A Watan Yuli
Dogo ya kuma bayyana cewa an kama mutum 76 da ke ɗauke da tutar ƙasar Rasha, ciki har da wani ɗan ƙasar waje, an samu bindigu kirar AK-47 guda biyu da wasu muhimmiyar dukiya a lokacin da ake gudanar da wannan aiki.
Bugu da ƙari, rundunar ta kama mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, da mutane biyar da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, da kuma mutane takwas da ake zargin masu satar motoci ne, tare da samun bindiga kirar Beretta.
Kwamishinan Ƴansandan ya sanar da cewa an ceto mutane 13 da aka yi garkuwa da su yayin gudanar da aikin. Duk waɗanda ake zargi za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.
Dogo ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da bayanan sirri don taimaka wa a kama masu aikata laifuka, tare da tabbatar da cewa rundunar tana aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin magance barazanar tsaro a jihar.