Mataimakin shugaban tawagar kasar Sin a gasar Olympics Zhou Jinqiang, ya bayyana a gun taron manema labarai da aka gudanar jiya Lahadi cewa, tawagar kasar Sin a gasar Olympics ta Paris 2024 ta samu mafi kyawun nasara a kasashen ketare tun bayan halartarta gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi a kasashen waje a shekarar 1984.
Zhou ya ce, Tawagar mai kunshe da ‘yan wasa 404 da suka fafata a gasanni 232 na wasanni 30, sun samu lambobin zinari 40 da azurfa 27 da tagulla 24. Adadin zinari da ta samu ya zarce zinari 39 da ta samu a gasar Olympics ta London, kuma ‘yan wasa 60 ne suka lashe zinari, wanda hakan ya kafa sabon tarihi na halartar wasannin Olympics a ketare.
Zhou ya kara da cewa, “Idan akwai kalma daya da za a takaita rawar da tawagar ta taka, to, “ci gaba ne”, a cewar Zhou, yana mai nuni da cewa, kasar Sin ta fafata a karin wasanni, kuma ta samu karin lambobin zinari, bayan da ta kara shiga gasannin masu tsanani.
Wasannin guda shida da kasar Sin ke da kwarewa, wadanda suka hada da wasan nutsewa, da wasan teburi, da kuma wasan daga nauyi, sun samu lambobin zinari 27, wanda ya kai kashi 67.5 bisa dari na jimillar, da kuma nuna kokarin da al’ummar kasar suka dade suke yi a fannin horaswa ta kimiyya. (Yahaya)