Hukumar kiyaye haɗurra ta kasa (FRSC), ta tabbatar da mutuwar mutane 16 a wani haɗarin mota da ya rutsa da su a kan titin Ojoo-Iwo na babbar hanyar Legas zuwa Ibadan yau Talata.
Kakakin hukumar na reshen jihar Oyo, Mayowa Odewo, ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a Ibadan, inda ya ce wasu mutum 17 sun samu raunuka daban-daban a haɗarin.
- Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Karin Albashi Da Alawus-alawus Ga Ma’aikatan Shari’a
- Kakakin Majalisar Bauchi Ya Goyi Bayan Sukar Tinubu Da Gwamnan Jihar Ya Yi
Ya ce mutane biyu ba su samu rauni ba daga cikin mutane 35 da suka haɗa da maza 14 da mata 10 da yara mata da maza 11 duk da hadarin ya rutsa da su wanda aka alakanta da ƙwacewar birkin wata babbar motar.
Sauran motocin sun haɗa da motar yan kasuwa ƙirar Nissan da ƙaramar tasi kirar Nissan Micra da kuma Honda Accord wanda tuni aka garzaya da mutanen 17 da suka jikkata zuwa asibiti da ke kusa don kula da lafiyarsu inda da aka miƙa gawarwakin sauran ga ‘yansanda.
Kakakin ya yi kira ga direbibi da su guji tuƙin ganganci tare da kula da ababen hawa yadda ya kamata don kiyaye asarar rayuka daga hadurran ababen hawa da za a iya kaucewa.