Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga sukar da Gwamna Bala Mohammed ya yi kan manufofin tattalin arzikin Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu.
A lokacin kamfen ɗin jam’iyyar PDP don zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Bauchi, Gwamna Mohammed ya nuna damuwarsa game da tattalin arzikin ƙasa, yana zargin Gwamnatin tarayya da aiwatar da manufofin da suka haifar da ƙaruwar talauci, da yunwa, da matsin tattalin arziƙi a faɗin Nijeriya.
- Ba Wanda Zai Yi Zanga-zanga A Bauchi – Muhammad Ibrahim
- Gwamna Bala Ne Ya Jefa Al’ummar Bauchi Cikin Matsin Rayuwa Ba Tinubu Ba – Sanata Shehu Buba
A wata sanarwa da ya fitar, kakakin majalisar Suleiman ya jaddada waɗannan ra’ayoyi, inda ya bayyana cewa tasirin waɗannan manufofin na yin illa ba kawai a jihar Bauchi ba, har ma a duk faɗin ƙasa.
Ya bayyana cewa sukar da gwamnan ya yi ya yi ne duba da halin ƙunci da ake ciki, kuma ya yi kira ga shugabanni da su tsaya tsayin daka don tabbatar da aiwatar da manufofin da ke fifita jin daɗin jama’a.
Suleiman ya yi kira da a sake duba manufofin Gwamnatin tarayya don tabbatar da cewa manufofin da ake aiwatarwa masu ɗorewa ne kuma suna amfanar da mafi yawan jama’a.
Kakakin Majalisar ya kuma yi kira ga sauran shugabanni da su haɗa kai wajen kira da a sake nazarin waɗannan manufofin, yana mai jaddada cewa jin daɗin al’umma ne ya kamata ya zama ginshiƙin kowace gwamnati.