‘Yansanda sun kama wani mutum mai suna Haruna Musa, mai kimanin shekara 21, yana lalata da mahaukaciya a Ungwar Gwari Kwamba, karamar hukumar Suleja ta jihar Neja.
A wani faifan bidiyo da jaridar Daily Trust, ta samu, an ji Musa yana cewa, bai kai ga samun gamsuwa ba kafin asirinsa ya tonu.
An kama Musa, da wani ganye wanda ake kyautata zaton tabar wiwi ce, wadda yake sha har ta kawar masa da hankalinsa, wadda ya debo daga kauyensu.
Ya ce; “In ban da asirina ya tonu na tabbatar da sai na sadu da wannan mahaukaciya. Ban san yadda aka yi aka gano ni ba. Don haka ina rokon ku yi min afuwa.
Ni yaro ne, ina da abubuwa masu yawa da zan bayar da gudummawa a kansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp