Ga wanda ke sha’awar fara kiwon Kajin gida, yana iya farawa da kamar guda 20; an fi kuma so a fara cikin watan Agusta, ta yadda kafin karshen wata 12 na shekarar; ya tara Kaji sama da 300.
Ga masu son samun bayanai a kan yadda ake kiwon Kajin gida, ga wasu daga cikin bayanai da wasu kwararru a fannin kiwon Kajin suka bayyana kamar haka:
Ka sayi Kajin gida kamar guda 20 da suke gab da fara yin Kwai da kuma balagaggun Zakaru kamar guda uku.
A koda-yasuhe, ana so a rika ajiye Zakara guda daya ga matan Kajin gida kamar daga bakwai zuwa goma, domin su yi saurin daukar Kwai tare kuma da tabbatar da Kwan ya kai munzalin kyankyashewa.
- Suna fara yin Kwai A cikin wata guda
- A wata na biyu kuma suke fara yin kyankyasa
- ‘Yan tsakin na fara girma a cikin wata na uku
Kazalika, matukar ‘yan tsakin sun kai munzalin wata guda, ba sa bukatar ci gaba da jin dumin uwarsu.
Haka nan, idan ‘yan tsakin suka kai wata daya, a nan ana bukatar a janye uwar daga jikinsu, sai ka ci gaba da kiwon su da kanka har sai sun kai tsawon wata biyu ko sama da haka kafin ka fara kyale su su ci gaba da rayuwarsu da kansu.
Daukar wannan matakin, zai kasance kamar tilasta wa Kazar ne fara saka wasu Kwaikwayen.
A cikin wata na hudu, Kazar ta kan dauki hutu ne domin sabawa da rashin zama da ‘ya’yan nata da ta kyankyashe.
Har ila yau, cikin wata na biyar; Kazar za ta fara yin wani sabon Kwai. A cikin wata na shida kuma, Kazar za ta sake kyankyashe wani sabon Kwan.
A wata na bakwai, za ta fara renon ‘ya’yan da ta kyankyashe, wanda hakan zai zama tamkar kara maimaita yadda aka zayyana a baya ne.
Wasu daga cikin abubuwan da ya kamata mai kiwon Kajin gida ya lura da su sun hada da:
1-Yin gwajin a kan Kaza daya sau biyar kafin ta kai ga gajiya.
2-A duk zagaye daya, idan har ka ci gaba da yin haka zuwa mako guda; Kazar za ta rika kyankyasa a duk kwana 21.
3-Ana so a rika sanya Kwai takwas a kowane kwanci daya da Kazar za ta yi, wanda a wani lokacin za ta iya kyankashe takwas din baki-daya; inda kuma a wata kyankyasar maras inganci, Kazar za ta iya kyankyashe Kwai bakwai ne kadai.
Haka zalika, kar ka kasance mai zalama; domin Kazar na da sararin yin kyankyasar har Kwai takwas din, sabanin guda 10 wanda a karshe Kwan zai iya lalalacewa.
4- Idan ka samar wa ‘yan tsakin muhalli mai kyau, wanda ya kasance nesa da inda Maguna da sauran kwarin za su iya halaka su, za ka iya samun balagaggun Kaji biyar a duk kyankyasa daya.
5- Idan har ka iya kiyayewa ka samu Kajin biyar, a duk Kwai guda takwas da suka kyankyashe maka, za ka iya samun Kaji guda 20 tare da kuma samun karin wasu sabbin Kajin guda 100 a zagaye na farko.
6- Idan Kazar ta yi kyankyasa ne a karo na farko cikin shekara daya, ‘yan tsakin da ta kyankyashe a zangon farko, su ma za su iya fara yin nasu kyankyasar.
7- Misali daga Zakara 50 zuwa Kaji masu yin Kwai 50. Hakan zai iya ba ka Zakaru 150 da kuma Kaji masu yin Kwai 150.
8- Idan ka sayar da balagaggun Kaji guda 100 a kasuwa, hakan zai sa ka kara samun kasuwa.
A dukkanin wadannan abubuwa da aka zayyano a sama, burin dai shi ne kokarin samun kudaden shiga.
Kar ka damu kanka wajen kallon yawan aikin a yanzu, amma ka duba yawan sakamakon da za ka samu.
Bugu da kari, Kazar gida na iya yin Kwai daga 15 zuwa 18 kafin ta kai ga ta fara kyankashe su.
Abin da yake da muhimmanci shi ne, ciyar da su abinci tare da samar musu da ruwan sha da kuma duba lafiyarsu akai-akai; don kare su daga kamuwa da cututtuka.
Majiya: Dandalin ‘Mind On Matters’