Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai. Assalamu alaikum.
Ya ku ‘yan uwana masu daraja, masu albarka ‘yan Arewa! Ku sani, har gobe ruwa yana maganin dauda. Har gobe Arewa Arewa ce. Har gobe, ko da goma ta lalace tafi biyar albarka. Mu har gobe Arewar mu Arewarmu ce. Bamu da inda yafi ta duk duniya. Babu wani wuri da muke so da kuma kauna fiye da ita. Don haka, kar ku taba yarda a sare maku gwiwa. Kar ku taba yarda a bata maku ginshikin ku.
Duk yadda wasu ‘yan kudu za su soki Arewa, duk yadda zasu Bata ta, duk yadda za su kushe ta, duk yadda za su yi wasu maganganu na shirme, maganganu na cin mutunci, maganganu na batanci akan Arewa, wallahi babu wanda zai iya sa mu kalli Arewa da wani mummunan kallo. Su ma sun sani, Arewa ba kanwar lasa bace. Sun sani, ba’a iya yi sai da Arewa. Sun sani, dan Arewa yafi karfin raini da wulakanci.
Idan kun lura da kyau, zaku ga wasu marasa kishi, ‘yan uwanmu ‘yan Arewa, suna ta famar ture-turen wasu rubuce-rubucen ‘yan kudu, wanda suka yi suka soki Arewa da ‘yan Arewa, akan wannan zanga-zanga da ta faru, wai suna kafa muna hujja da wadancan rubutuce- rubucen. To muna kira ga ‘yan Arewa, su yi watsi da wancan shirmen, suyi watsi da irin wannan hali na karantawa, da wadancan ‘yan uwan mu suka dauka.
Mu mun fi karfin a razana mu da rubutun wasu mutane. To ma wai yau ne suka fara rubuce-rubucen nasu na batanci akan Arewa da ‘yan Arewa, bare har rubutun su ya razana mu, ko ya bamu tsoro, ko ya tayar mana da hankali?
Don haka duk wasu rubuce-rubucen da za su yi, saboda kawai an yi zanga-zanga a Arewa, mu wannan kallon su muke yi a matsayin masu shirme, masu bata lokacin su a banza. Kuma ai ma sun samu masu goyon baya ne daga wasu ‘yan Arewar, na aci mutuncin Arewa da ‘yan Arewa, shi yasa suka samu damar yin wasu rubuce-rubucen banza da wofi, rubuce-rubucen iska da shirme, rubuce-rubuce marasa kan gado. Yo dama kai dan Arewa kana tsammanin su rubuta wani abin arziki a kan ka? To idan wannan shine tunaninka, ka sani ka makaro. Don haka, mu a tunanin mu, duk wani rubutu na batanci da ‘yan kudu za su yi akan Arewa, wannan ba sabon abu bane. Mu kawai bakin cikin mu, bai fi wadanda aka samu daga Arewar, suna goya masu baya ba.
Ai dan Arewa wallahi idan ba’a yaba masa ba a kasar nan, to kuwa ba za’a zage shi ko a hantare shi ba. Don girman Allah wane irin hakuri ne dan Arewa bai yi ba a kasar nan? Wane irin cin kashi ne ba’a yiwa ‘yan Arewa ba a mulkin kasar nan? Sannan shin ma wai don Allah a Arewa ne aka fara yin zanga-zanga a kasar mu Nijeriya?
Idan ana maganar daga tutar wata kasa, duk mai bibiyar ayyukan ‘yan kungiyar IPOB a Nijeriya, na yankin inyamurai, ya san da cewa babu ranar da IPOB ba za su daga turar kasar Isra’ila ba. Sannan domin Allah a cikin kasahen da suke taimakawa kabilar Inyamurai, suka yakki Nijeriya, a lokacin yakin basasa, babu kasar Isra’ila ne?
Sannan a lokacin da aka yi zanga-zangar ENDSARS a kasar nan, don Allah wace tuta suka daga? Kowa ya kalli irin yadda suke yawo ko’ina a garuruwansu, suna kaga tutar kasar Amerika. Amma don me yasa bamu ji an taba ayyana cewa wannan cin amanar kasa ba ne, wato sai yanzu da yazo akan Arewa da ‘yan Arewa ko? Kawai don an raina mu ne, don an raina mana wayo, an raina mana hankali, an dauke mu ba ‘yan kasa ba, an dauke mu marasa wayo.An dauke mu bakin-haure ko?
Don Allah wane irin kone-kone, da sace-sacen dukiya, da kashe-kashe, da fasa shaguna ne ba’a yi ba a zanga-zangar ENDSARS, lokacin mulkin Buhari? Amma daga karshe, ba manyan su bane da wasu kasashen duniya, suka daure masu gindi, suka ce an zalunce su, har kotu aka je, daga karshe aka sanya gwamnati ta biya wasu kudade ga wasu mutane da suka yi zanga-zangar ENDSARS?
Kuma wai har an samu wasu daga cikin mu, idon su ya rufe basu hango gaskiyar lamurra.
Mu ‘yan Arewa, babu ruwan mu da kabilanci, domin ba shi muka sa a gaba ba, amma mun ga rainin wayon yana neman yayi yawa ne, shi yasa kuka ga muna yin duk wadannan bayanan.
A yau, a kasar nan, muna gani kiri-kiri, shugaban kungiyar yarbawa zalla ta OPC, wato Ganiyu Adams, babu irin ta’addancin da bai yi ba a kasar nan. Babu irin barnar da basu yi ba, amma an wayi gari yau shi ne abin girmamawa ne a wurin mutanen sa. Sun tsaya masa, sun daure masa gindi, manyan yankinsa suna tare da shi, basa zagin sa, basa hantarar sa, basa wulakanta shi, basa ci masa mutunci, kai daga karshe ma har sarautar gargajiya suka bashi, ta sarautar ARE ONA KAKAMFO, sarautar da ba’a baiwa kowa ita, sai wanda yake jarumi, hamshaki, babban mutum a cikinsu. Kaje ka binciki tarihi da matsayin wannan sarautar da aka bashi.
Yau a yankin kasar Ibo, muna kallon irin yadda suka dauki Mazi Nnamdi Kanu, dan gwagwarmayar samun kasar Biyafara. Wallahi Nnamdi Kanu ya fi duk wani dan siyasa, ya fi duk wani mai kudi, ko mai sarauta, a yankin kasar Ibo baki daya, kuma ba don komai ba, kawai don yana gwagwarmayar neman ‘yanci masu ‘yanci, kamar yadda suke kallo. Don Allah, wace irin barna ce basu yi ba a kasar nan? Wane irin ta’addanci ne basu yi ba, da sunan kwatar ‘yanci? Amma an wayi gari, tun daga Sarakunansu, har zuwa ‘yan siyasar su, har zuwa masu arzikinsu, duk sun tsaya masa, akan su sam ma ba su yarda cewa shi mai laifi ba ne, kuma suna nan suna ta fadi-tashin ganin lallai sai gwamnati ta sake shi. Wannan kawai duk a takaice ke nan fa.
Sannan ina Sunday Igboho, dan gwagwarmayar tabbatar da kasar yarbawa zalla? Wane irin zagi da cin mutunci ne bai yiwa kasar nan ba? Wane irin zagi da cin mutunci ne bai yiwa kabilun Hausa-Fulani ba? Wane irin ta’addanci ne bai yi ba, da sunan kafa kasar kabilar yarbawa zalla? Amma an wayi gari, wannan mutum ya zama babban jarumi a cikin su, ya zama abin girmamawa. Ka tafi gidan sa, ka ga yadda ‘yan siyasar su, da Sarakunan su, da masu kudin su, kai da kowa na su, har da malaman addinin su, ka ga irin yadda suke kai masa ziyara, suna girmamawa shi. Sun dauke shi wani irin babban jarumi, suna bashi kariya, fiye da yadda kake zato. Har kama shi an yi, aka tsare shi, amma manyan su da ‘yan siyasar su, da Sarakunan su, da masu kudinsu, wallahi duk sun bayar da gudummawa wurin kubutar da shi.
Ka tafi yankin Neja Delta, ka ga yadda ‘yan gwagwarmayar kwatar ‘yancin su suka zama wasu irin hamshakai, abin girmamawa a cikin al’ummar su. Za ka ga irin girman da ake ba su ya fi na Sarakuna, yafi na masu arziki, da ‘yan siyasa. Sun yi kudi na fitar hankali, fiye da yadda ake zato.Wasu daga cikin su ma har kwangiloli masu tsoka ake basu daga gwamnati, irin su Tampolo, irin su Mujahid Asari Dokubo , da dai sauransu. Wasu ma duk an kai su kasashen waje sun yi karatu, sun koyi sana’oi kuma daga baya gwamnati ta basu aikin yi.
Wadannan fa duk na kwana-kwanan nan ne, ban da wadanda suka wuce a can da. Kuma wannan duk ina kawo maku sune a takaice.
Amma abin bakin ciki shine, da ka zo yankin mu na Arewa mai albarka, zaka tarar abin ba haka yake ba. Su su zage ku, wasu ‘yan uwanka ma ‘yan Arewar su zage ku. Abin ya zamarwa matasan Arewa da talakawansu da al’ummar Arewa baki daya, GABA KURA BAYA SIYAKI.
Matashin Arewa a yau, an wayi gari ya rasa inda zai sa kansa. Ya rasa mafita. Ya rasa wanda zai kama hannunsa yace masa, kai wannan daidai ne, wannan ba daidai ne ba.
Talakawan Arewa da matasanmu da al’ummarmu, an hana su noma da kiwo da sana’o’in da suka saba yi, sun rasa inda za su sa kawunan su, saboda mummunan rashin tsaro da yake addabar mu, kuma sun fito domin su nuna damuwar su akan hakan, saboda kawai an samu kuskure, saboda wasu miyagun mutane da aka yo haya, sun shiga, sun bata masu lamari, shine sai su zama abin zagi, abin cin mutunci da hantara? Sam ba zata sabu ba, wai bindiga a ruwa!
Eh, dukkanin mu mun yi ittifaki cewa, tashe-tashen hankula, kone-kone, kashe-kashe, da sace-sace, da fasa shaguna, da zubar da jinin bayin Allah duk abubuwa ne marasa kyawu, abubuwa ne da ba su dace ba, wadanda matasan mu, talakawa suka yi da sunan zanga-zanga.To amma don girman Allah, idan zamu yiwa kan mu adalci, sai mu tambayi kawunan mu, me ya jawo faruwar hakan? Shin da ace hukumomi sun kula da hakkin matasa da talakawa, yadda ya dace, da hakan ai bata faru ba ko?
Kuma ku duba ku gani fa, ‘yan Arewa a yanzu suna cikin tsaka mai wuya ne. Domin idan ba’a yi hankali ba, idan bamu yi hattara ba, yadda shekaru takwas din shugaba Buhari suka zamar wa ‘yan Arewa marasa amfani, yanzu ma fa haka muke hange a cikin wannan mulkin fa!
Kuma ya kamata mu kara sani, ba wani abu bane matsalar Arewa ba illa, rashin hadin kai, yi ma juna hassada, cin dunduniyar juna, rashin girmama fahimta da ra’ayin juna.Rashin son ci gaban juna, kokarin kwarewa juna baya, sannan babban laifin shine, hada kai da ake yi da wasu daga cikin ‘yan Arewar, domin aci amanarta da ta ‘ya’yanta.
Don haka, da yardar Allah, mu ba zamu gushe ba muna addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala, akan matsalolin da suke damun mu a kasar nan da kuma yankin Arewa. Zamu ci gaba da fadawa Allah yayi mana maganin duk wasu masu zaluntarmu a kasar nan!
Zamu ci gaba da addu’a da rokon Allah, duk wanda yake da hannu cikin kawo mana rashin tsaron a Arewa da Nijeriya baki daya, Allah yayi mana maganinsa. Duk wanda yake murkushe kudin da ake warewa domin samar da tsaro, yana sha’anin gabansa, Allah yayi mana maganinsa. Duk wanda yake hada baki da ‘yan ta’adda, ana sace mu, ana kashe mu, ana zubar da jinin mu, ana hana mu noma da kiwo da sana’o’i, Allah yayi mana maganinsa. Duk wani azzalumin dan kasuwa da yake da hannu wurin haifar da tashi da hauhawar farashin kayayyaki, babu gaira babu dalili, Allah yayi mana maganinsa. Duk wani shugaba a cikin wannan al’ummah, wanda baya tausayinmu, Allah yayi mana maganinsa. Duk wanda yake da hannu wurin kwashe kudin talakawa, yana jin dadi daga shi sai iyalansa, da duk masu taimaka masu, Allah yayi muna maganinsu. Duk wani azzalumi da yake kan mulki, da duk wani azzalumi da yake cikin daji, da na cikin gari, suna cutar da al’ummah, Allah yayi mana maganinsu. Allah ya isar mana, Allah ya saka mana ga duk wani mugu, azzalumi, amin Ya Hayyu Ya Kayyum, Ya Zal Jalali Wal-Ikram!
Allah ya sawwake, amin.
Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuta, daga Okene, Jihar Kogi