Masana da masu ruwa da tsaki a lamuran da suka shafi noma sun bayyana muhimman dalilin da suka sabbaba Nijeriya ke tsintar kanta cikin matsalolin karancin abinci.
Masanan sun ce a baya dai, bangaren noma shi ke jan ragamar tattalin arzikin Nijeriya, yayin da manoma a jihohi da shiyyoyi suka maida hankali ka-in-da-na-in wajen noma kayan abinci a yankunansu da hakan ya bayar da damar wadata garuruwansu da kayan abinci har ma su fitar zuwa waje.
- Nazari Kan Samun Kudin Shiga Ta Hanyar Kiwon Kajin Gida
- Masana Sun Nuna Damuwarsu Kan Yadda Ake Takura Wa Masu Zuba Jari Da Ka’idoji
Sun kuma yi la’akari da yadda manoman arewa suka fi kwarewa wajen noma shinkafa, masara, gyada kuma wadannan abincin ana samar da su sosai, wadanda su ne ma aka fi amfani da su, yayin da a kudu maso yamma kuma suka gwanance wajen noman koko da rogo, inda yankin kudu maso gabas suka rungumi samar da manja.
A cewar masanan, kasar ta samu kanta cikin cin gajiyar wadannan abubuwan da ake noma, amma yanzu lamarin na neman zama babbar matsala, inda ake samun karancin abinci, yayin da manoma da dama suka daina noma, kamfanoni su na fuskantar karancin samun kayayyakin amfani, sannan ita kuma gwamnati ta dukufa wajen yaki da matsalar tsaro da rigingimun siyasa.
Shugaban kungiyar manoma ta COMAFAS, Dakta Austine Maduka, ya ce, samun danyen mai da ake yi a Nijeriya ya sanya kasar ta sakankance da lamarin samar da kayan noma, inda ya ce, hakan kuma ya janyo matasa da dama sun bar garuruwansu da ke kauyuka domin zuwa birane neman aiki a bangaren mai da iskar gas, yayin da suka bar harkokin noma kuma.
Ya kuma nuna cewa rashin nagartattun tsare-tsaren gwamnati kan noma sun kara shafan lamarin samar da kayan abinci. Ya nuna takaicinsa, kan yadda shugabannin da aka yi a Nijeriya ba su iya ci gaba da tafiyar da tsare-tsaren shugabannin da suka karbi mulki a hannunsu, inda ya nuna cewa kowani shugaba ya zo sai ya ce zai yi nasa tsarin daban, yayin da hakan ke maida hannun agogo baya.
Ya kuma nuna cewa wasu shugabannin sun fi maida hankali kan nau’ikan kayan abinci da ake cirewa a arewa, yayin da wasu tsare-tsaren gwamnatocin baya kuma suka fi daukan hankali a irin kayan abincin da ake nomawa a kudanci.
Kazalika, ya nemi gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar ruwa da ta bude wasu karin dam-dam da manoma za suke samun ruwa a kowace shekara yadda suke bukata. Ya ce, kacokam an dogara ne kawai da noma in an samu damina, yayin da noman rani kuma ba su da yawa.
Ya ce, ya kamata gwamnati ta tanada ruwan da ke malala a kasa, musamman wanda yake zama ambaliya ta yadda manoma za su samu na amfani da shi bayan damina, sannan ta kara samar da filayen noma a jihohi da kananan hukumomi.
Sai ya nuna cewa wasu gwamnonin su na kokari sosai wajen taimaka wa harkokin manoma da dukkanin abubuwan da ake bukatu a bangaren noma, ya buga misali da Jihar Jigawa, ya ce kokarin da gwamnatin Jigawa ke yi a bangaren noma za a ga alfanunsa nan gaba.
Ya ce, gwamnatin Inugu da Anambra su ma a kwanan nan sun rabar wa manoma da iri da kayan noma. Ya ce, akwai bukatar gwamnatoci su sanya a ransu wajen maida hankali kan yadda za a yi noma da yadda za a girbe amfanin noma.
A nasa bangaren, kwararre kan noman rogo daga Jihar Ogun, Kunle Abdul ya soki gwamnatin jihar da rashin kyawawan tsare-tsaren da za su ciyar da harkokin noma gaba, inda ta kasa koyi da yunkurin gwamnatin tarayya na inganta harkokin noma.
Shi kuwa, kwararre kan abinci da wadatar abinci, Hammed Jimoh ya ce, manyan matsalolin da Nijeriya ke fuskanta a bangaren samar da abinci sun hada har da matsalar rashin tsaro da ya janyo salwantuwar manoma da dama a kasar nan, musamman a jihohin Borno, Benuwai, Zamfara, Kaduna da sauran jihohi, lamarin da ke kara sanyawa wasu manoma kaurace wa gonakai domin tsira da rayukansu.
“Idan kuka nazarci yankunan da matsalolin tsaro suka fi kamari a halin yanzu a Nijeriya, za a fahimci jihohin nan su ne masu samar da abinci mafi yawa a baya, kamar jihohin Borno, Katsina, Kaduna da Benuwai.”
Jimoh ya kuma ce sauyin yanayi shi ma na barazana ga wadatar samar da abinci a Nijeriya, “An fi dogara da ruwan damina wajen noma a Nijeriya, sauyin yanayi na canzawa. An gaya min cewa kudu maso yamma kusan sama da watanni biyu ba su samu ruwan sama ba, don haka yanayin na canzawa.
“Muddin in za mu dogara kacokam kan sai mun samu ruwan sama mu yi noma, gaskiya za mu yi ta samun matsala, saboda ba za mu dunga samun abun da muke so ba, yana da kyau a nemo wasu hanyoyin na daban.”
Wani manomi a Jihar Kogi, Sunday Audu ya zargi gwamnatin da kin taimaka wa manoma balle manoma su samu kyautata nomansu.