Shafi ne da ya saba zakulo muku marubuta litattafan Hausa daban-daban manya da kananan domin jin ta bakinsu game da abin da ya shafi rayuwarsu da kuma rubutunsu, haka kuma shafi ne da ya saba kawo muku sharhin littattafan Hausa wadanda suka shude har ma da wadanda ake wallafa su a yanzu, inda a yau shafin ke tafe da tattaunawa da wata bakuwar marubuciyar FATIMA MUHAMMAD GURIN wacce aka fi sani da FATIMA GUREEJO. Ta bayyana wa masu karatu kadan daga cikin tarihin rubutunta har ma da irin nasarar da ta samu game da rubutu tare da wasu bayanan masu yawa. Ga dai tattaunawar tare da AISHA IDRIS ABDULLAHI (ALEESHAT) kamar haka:
Bari ki fara da gabatar wa masu karatu da kanki…
Sunana Fatima Muhammad Gurin wacce aka fi sani da Fatima Gureenjo.
Yaya dan takaitaccen tarihinki ya kasance?
Ni haifaffiyar garin Adamawa ce, nayi firamare da sakandare dina a garin Gurin, kana na tafi Katsina nayi karatun aikin jinya yanzu haka na kamalla har na Fara aiki a garin Gurin dake Adamawa.
Me ya ja hankalinki har ki ka fara rubutu?
Tarihin rubutuna tarihi ne me tsawo kuma me ban dariya, a gaskiya na fara karatun littatafai tun ina aji uku na firamare sanadiyar kakata da ke karanta littatafai a lokacin a littafi ake rubutawa, takan aike ni in karbo mata ‘renting’ wato hayar littatafai, to a duk sa’ar da na karbo mata in ta bani in mayar sai na boye na karance tsab sai in mayar in karbo mata wani, to a gaskiya tun daga nan na fara sha’awar in na girma in zama marubuciya, saboda abubuwa da yawa da nake tsinta a lokacin duk da kankantar shekaruna, a kan littafi ba irin dukan da ban ci ba daga karshe dai na samu nasarar daura Alkalami a shekarar dubu biyu da sha tara (2019) sanadiyar kadaici. Kasancewar muna da nisa kwarai daga Katsina zuwa Adamawa hakan ta sa a wani hutun karamar sallah ban iya na koma gida ba, to a sanadiyar wannan zama na fara rubutu.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Ba zan ce na sha wani gwagwarmaya ba duk da na fara ne a lokacin da ba wai na iya Hausar bane sosai, sannan ba ni da masaniya kan ainihin ita Adabin Hausar da dai sauransu, amma Alhamdu lillah na hadu da mutanen kirki cikin marubuta kuma sun taka muhimmiyar rawa wurin tallafa min suna kuma kan takawa har yanzu da nake kokarin tsayuwa kan kafafuwana.
Ta yaya kika sanar da iyaye lokacin da za ki fara rubutun ganin yadda kika sha duka a baya?
A gaskiya a lokacin da na fara rubutu ban sanar da iyayena batun fara rubutuna ba, amma da tafiya ta yi tafiya sun zo sun sani duk da mahaifiyata ba ta wani maida hankali kan littatafan Hausa ba ta bani goyon baya dari bisa dari, kalamanta kuma na “ki rike tarbiyyar gidanku da mutuncin mu iyayenki kuma ki rubuta abun da kika san ko a ranar gobe aka tambaye ki za ki iya ba da amsa a kai” da su nake amfani har yanzu kuma har abada in har zan dora alkalami kan Littafi da su zan cigaba da anfani.
Shin kin nemi taimakon wani ko wata kafin ki fara rubutu?
Kan na dora alkalamina da nufin rubutu na fara tuntubar marubuciya Aunty Ayusher mohd kuma sosai ta dora ni a hanya wadda a sanadiyarta na hadu da Aunty Bilkisu Musa Galadanchi wacce aka fi sani da (Aunty Billy) shugabata har yanzu a duniyar rubutu, sanadiyarta kuwa na hadu da marubuta masu tsananin kirki da karamci.
A yanzu za ki kamar shekara nawa da fara rubutu?
Akallah dai yanzu na kwashi shekaru shidda haka a duniyar marubuta.
Kamar wane irin labari ki ka fi mayar da hankali a kai wajen rubutawa?
A gaskiyar zan ce na fi yin rubutun da ya shafi soyayya, kaddarar rayuwa da dai sauransu.
Wane labari ki ka fara rubutawa kuma ya karbuwarsa ya kasance ga masu karatu?
Littafin da na fara rubutawa a rayuwata shi ne ZAHRA, duk da a lokacin babu wani cikakken ilimin kan rubutu amma wallahi Alhamdu lillah ya samu karbuwar da ban taba zato ko tsammani ba, a hostel namu har zuwa ake ana nuna ni. Alhamdu lillah.
Kin rubuta labari sun kai kamar guda nawa?
Na samu nasarar rubuta littatafai kamar guda Tara haka, a cikinsu akwai; Noor iman, Lelewal (farin wata), Gamon jini , Diddigar ƙaya, Igiyar rayuwa, da dai sauransu.
Cikin labarun da ki ka rubuta wanne ne ya zamo bakandamiyarki?
A gaskiya ba zan ce ga littafin da ya kasance bakandamiyata ba, saboda duka littatafai na ina matukar kaunarsu, duk cikinsu akwai tarin ilimin rayuwa daban-daban.
Wane labari ne cikin labarun da ki ka rubuta ya fi baki wahala?
Na fi shan wahala wurin rubuta littafin Lelewal (farin wata) saboda ya kunshi bincike me zurfi, binciken da ya shafi likitanci, garuruwa waenda da yawa ma ban taba ko mafarkin zuwa ba, da kuma sarkakiiya wacce ni kaina na sha wuya wurin warware shi.
Wadanne irin nasarori kika samu game da rubutu?
Alhamdulillah ai ko wannan hirar da nake nasara ce mai girma, idan ba don rubutun ba ai da ba zan kai ga isowa nan din ba, Sannan a ganka ma a nuna an san ka a kuma yi maka addu’a da fatan alkhairi babbar nasara ce wadda duk sanadiyar rubutu na samu hakan.
Ko akwai wani kalubale da kika taba fuskanta game da rubutu?
Gaskiya ban fuskanci ko wani kalubale daga marubuta ba, sai ma tallafawa da tarin ilimi dana kwasa kuma nake kan kwasa daga cikinsu.
Shin kin taba buga littafi?
A’a! Amma ina fata zuwa nan gaba in Allah ya ba ni iko.
Ko kin taba yi wa littafi kuka sanadiyyar karantawa?
Kuka kai, kasancewata me saurin kuka gaskiya da wuya in karanta littafi in gama ba tare da na zubar da hawaye ba, lokuta da yawa a nawa rubutun ma na kan dakata in yi kuka na ma’ishi kan in cigaba.
Wacce marubuciya ce ta fi burge ki?
Marubuta dai [murmushi!]… Marubuta da yawa suna burge ni ciki akwai: Sa’adatu Waziri Gombe, Halima Abdullahi K Mashi, Bilkisu Musa Galadanchi, Ayusher mohd, Mrsjmoon, Rufaida Umar, Safiyya Abdullahi Musa Huguma, da dai sauransu.
Su waye kawayenki a cikin marubuta?
Ina da kawaye da yawa a marubuta kaman su; Aisha Idris Abdullahi (Aleesha), Sadeey, ‘yar lelen royal star, Safiyya Galadanchi, Aunty Halillos da dai sauransu.
Kamar wane irin lokaci ki ka fi jin dadin yin rubutu?
A gaskiya na fi jin dadin rubutu bayan Magrib zuwa Isha ko bayan sallar Asuba, saboda a lokacin na kan zama cikin natsuwa, shiru da rashin hayaniya to ina jin dadin rubutu a irin lokutan.
Bayan rubutu kina yin sana’a?
Babu wata sana’a da nake yi gaskiya.
Wacce shawara za ki bawa makaranta har ma da marubuta?
Shawarata ga makaranta ita ce; Su kasance masu yi wa marubuta uzuri a rayuwa, kamar yadda suke da ‘personal life’ haka marubuta ma ba wai rubutu ne kawai aikin marubuci ba, yana da iyali, yana da aiki, yana ciwo kuma yana kuskure don marubuci mutum ne kaman kowa. Wannan uzuri dai shi nake roko ga makaranta da su dinga yi mana a koyaushe. Marubuta kuwa ina rokon mu da mu tsaftace alkalumanmu, mu ji tsoron Allah mu sani duk abun da ka rubuta zai zama shaida a kanka a ranar gobe walau alkhairi ko akasin haka.
Me za ki ce da makaranta wannan shafi na Adabi, har ma da ita kanta LEADERSHIP Hausa?
Ina godiya da lokutan ku da kuka bayar wurin bin wannan hira ta mu, ku kuma gidan jaridar Leadership Hausa ina yi muku fatan alkhairi da cigaba me dorewa.