Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon cikin wani sabon shirinmu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata, inda yau za mu yi bayani kan yadda ake hadin gasasshen Burodi da hade da kwai da madara.
Ga kayan da ya kamata a tanada domin hadi:
Burodi, Madara, Kwai Tattasai Ko Taruhu, Albasa, Magi, Gishiri da kuma Kori.
Ga Yadda Za a Hada:
Da farko za ki samo Burodinki amma ba mai yanka-yanka ba babba guda daya, sannan ki yayyanka shi ki ajiye a gefe, sai ki kada kwai daidai yawan da zai isheki ki kada madara ki zuba a cikin kwan da kika fasa ki gauraya su, sannan ki zuba tattasai ko taruhu duk wanda kike so, idan kuma hadawa za ki yi duk za ki iya yi wanda dama kin gyara su kuma kin jajjaga, sannan ki zuba albasa sai ki dan zuba magi da gishiri da kori ki kada su gaba daya, sannan sai ki dora abin suya a wuta, idan ya yi zafi sai ki dan shafa mai a jiki saboda kar ya kone, sannan ki rika dauko Burodin da kika yayyanka kina tsomawa a cikin kwan da kika hada kina sawa a cikin abin suyar kina gasawa idan kasan ya yi sai ki juya saman ma ya gasu. Irin wannan hadin kwai da madara yana dadi sosai. Za ku iya sha da shayi. A ci dadi lafiya.