Hukumar yi wa ƙasa hidima ta NYSC, ta kori matasa ‘yan bautar ƙasa 54 da ke da takardun gama makaranta na bogi bayan da jami’ar Calabar ta tattaro tare da gabatar mata da bayanansu.
Darakta Janar na hukumar NYSC, Birgediya Janar YD Ahmed, ne ya bayyana hakan a birnin tarayya Abuja, inda ya ce za kuma su gurfanar da su a gaban kuliya don girbar abinda suka shuka.
- JAMB Ta Warware Dambarwar Kayyade Shekarun Shiga Jami’oi
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaron Zamfara 3
Hakan na daga ci gaba da ƙoƙarin hukumar na hana ɗaliban da ba su cancanta ba samun takardar shaidar yi wa ƙasa hidima ta NYSC, ka na ya ce wasu 19 daga cikinsu da tun farko suka yi rajista ta yanar gizo an hana su yin hidimar, sauran 4 kuma basu da cikakkun takardun da za a amince dasu.
Ya ƙara da cewa akwai ƙarin matasa 101 da suma ba su cancanta ba kasancewar ba su da cikakkun takardu wanda adadinsu yakai 178, kuma haryanzu ana kan bincike.
Da yake ƙarin haske, Janar Ahmed ya ce hukumar NYSC ba za ta bar wata kafa ba da ɓata gari zasu shigo don lalata mata ayyuka saboda haka ya zama wajibi a ci gaba da tsaftace shirin.