A cikin shekarun da suka gabata, huldar inganta tattalin arziki tsakanin Sin da Vietnam ta kasance bisa manyan muradun bangarori daban-daban. Kuma an kulla yarjejeniyoyi a fannonin bunkasa tattalin arzikin dijital, da hadin gwiwar samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da shawarar ziri daya da hanya daya (BRI), wanda ke nuni da tarin damammakin samun ci gaba ta bai daya.
Kasar Sin ta ci gaba da kasancewa babbar abokiyar cinikayyar Vietnam, kuma kasuwarta mafi girma ta biyu ta fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, kuma ta daidaita hanyoyin samun kayayyakin amfanin gona na Vietnam. Darajar cinikayyar kayayyaki tsakanin kasashen biyu ya zarce dala biliyan 200 a shekarar 2023, yayin da ake sa ran kamfanonin kasar Sin za su kara saka hannun jari a Vietnam. Babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kai wata muhimmiyar ziyara a kasar Vietnam a bara, wadda ta kara bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Shima babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta kasar Vietnam, kuma shugaban kasar Vietnam To Lam ya fara ziyarar aiki a kasar Sin, daga ranar 18 ga watan Agustan nan, kuma ita ce ziyararsa ta farko zuwa kasashen waje tun bayan hawansa karagar mulki, wadda ke nuni da muhimmancin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Alal misali, saurin zamanantar da jama’ar kasar Sin da bude kofa ga kasashen waje, ya tabbatar da alfanu ga tattalin arzikin kasar Vietnam, ya kuma taimaka wajen samar da makamashi mai sabuntuwa, da inganta samar da wutar lantarki da samar da ayyukan yi ga jama’ar Vietnam. Gamayyar hadin gwiwa ta kasa da kasa ta samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba ta BRI ta samar da karin damammaki don aiwatar da manufofin makamashi mai tsafta cikin sauri, yayin da yankunan masana’antu da yankuna na musamman na tattalin arziki ke ci gaba da jawo kaso mai girma na kamfanonin kasar Sin. Duk wadannan na haifar da damammaki don karfafa saka hannun jari kai tsaye daga ketare da kuma samar da ayyukan yi a masana’antu ta hanyar hadin gwiwa.
Dorawa akan ci gaban da aka samu kawo yanzu, anan sa ran ziyarar To Lam zai kara karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a matsayin wata alama ta dangantakar dake tsakanin Sin da Vietnam, da samar da sabbin hanyoyin shiga kasuwannin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, da kuma taimaka wa kasashen biyu su cimma matsaya daya mai karfi kan samun ci gaba tare. (Mohammed Yahaya)