Ci gaba daga makon da ya gabata
Kafin na ci gaba da tattauna abin da na fara a makon da ya gabata, Mallam Rabi’u Indabawa na jaridar LEADERSHIP HAUSA, ya nemi na yiwa masu karatu bayani kan banbance tsakanin ‘Ciniki da Kasuwanci’ to, abin da ake nufi da Ciniki shi ne tattaunawar da ake yi da mai saye da sayarwa a wajen kasuwanci.
Misali ka zo kasuwa ka ga kayayyaki iri-iri sai ka tambayi mai kayan nawa yake sayarwa, to wannan tattaunawar da za ku yi har a sami matsaya ka sa ya ka tafi shi ne ciniki.
Wato a takaice tattaunawa da ake yi da mai kaya da mai saye shi ne ciniki. Sannan kasuwanci kuma a nan nufin bukata, misali a hadu a wani guri da aka ware don saye da sayarwa ko kuma a cikin gida tun da ita kasuwa ba dole sai fili ko wani guri ba, a’a ita kasuwa tana nufin bukata, shi kuma wanda yake neman wannan abin da kai kake da shi sai ka zo ku yi yarjejeniya ka saya a wajensa ya sayar maka.
Wannan shi ne dan karin bayani da zan yi game da tambayar da Mallam Rabiu Indabawa ya yi, amma Allah ne masani. Kaima mai karatu idan kana da abin da zaka kara na bayani game da wadannan kalmomi muna maraba da gudumawarku.
A makon da ya gabata na yi tsokaci a kan menene kananan sana’oi da yadda rabe rabensu yake. Da fatan mai karatu ya fahimta an san inda wannan darasi namu ya sa gaba. Abin da nake so a kuma fahimta kuma shi ne na dauki wannan batu ne na kananan sana’oi domin mutane su fahimta cewa su irin wadannan kananan sana’oi su ne kashin bayan ci gaban duk wata kasa a duniya.
Saboda kamar yadda na fada a makon da ya gabata irin wadannan sana’oi ko kamfanoni su ne suke ba wa ‘yan kasa bila adadin aikin yi domin gwamnatocinmu ba za su iya ba wa kowa aiki ba.
Shi ne ya sa kasahen duniya a kullum suke kuma bijiro da abubuwa na jin dadi don tallafa wa irin wadannan sana’o’i ko masu sana’oi.
Miliyoyin kudade ko na ce biliyoyin kudade suna juyawa kullum a cikin irin wadannan sana’o’i, saboda haka ya wajaba a garemu da mu fadakar da jama’a yadda ya kamata su kuma rike sana’o’insu da mahimmacin gaske saboda su ne suke ba su abin da rayuwarsu take amfani da shi.
Idan za’a iya tunawa a shekarar 2020 annobar Korona ta yi wa duniya gaba daya wani mummunan kamu da kowa da kowa ya ji a jikinsa ciki kuwa har da masu kananan sana’o’i.
A kasashen duniya daban-daban sun bijiro da shirye shirye don tallafa wa irin wadannan sana’oi ta yadda suka rika fitar da kudade don biyan ma’aikatan irin wadannan sana’oi ko kamfanoni albashi.
Misali a Kasar Amurka, sai da aka shafe wata shida gwamnatin Amurka tana biyan kananan kamfanoni ko sana’o’i kudade saboda kada su daina samun kudin kashewa. Kuma sun yi hakan ne don kada wadannan sana’oi su tsaya su daina aiki, saboda idan sun tsaya mutane da yawa za su ji jiki.
Haka kuma dokar kulle da aka saka lokacin Korona ta taba sana’o’i da yawa a duniya ciki har da Nijeriya. Shi ne dalilin da ya sa kasashen duniyar suka kirkiri biyan kudaden albashi na musamman saboda kawai sun san cewa wadannan sana’oi ko kananan kamfanoni su ne suke tafiyar da tattalin arziki ko wace kasa a duniya.
Muma a Nijeriya gwamnati ta yi wannan kokarin na kirkiro da shirin ‘surbibal fund’ wato biyan kudi ga kananan ma’aikta da suke aiki a kmafanoni masu zaman kansu don rage radadin da hana fita da cutar Korona ta jawo wa al’ummar kasa.
Mutane da yawa a Nijeriya sun samu kyautar Naira 30,000 na kimanin wata uku wato Naira 90,000 a jumlace. Wannan kuma hakika ta sa mutane da yawa ‘yan Nijeriya sun sami sauki ta samun wannan kudaden.