Darakta mai lura da harkokin yammacin Asiya da nahiyar Afirka na ma’aikatar cinikayyar kasar Sin Shen Xiang, ya ce Sin na aiwatar da matakai daban daban na saukakawa kasashen Afirka matsin da suke fuskanta daga tarin bashin dake wuyansu.
Shen, wanda ya bayyana hakan a jiya Talata yayin wani taron manema labarai, ya ce karkashin tanadin shirin dage basuka na kungiyar G20, Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa kasashen da lamarin ya shafa kaiwa ga yarjejeniyar dage musu bashi.
Kaza lika, jami’in ya ce karkashin tsarin hadin gwiwa na dandalin hadin kan Sin da kasashen Afirka ko FOCAC, Sin ta yafe basukan da take bin wasu kasashen Afirka, ta hanyar kawar da kudin ruwa dake kan lamunin gwamnati kafin cikar wa’adin biyansa a shekarar 2021. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp