Na rasa dalilai kwarara da suka janyo al’adunmu na kwarai suka shude na rashin girmama shugabanni: Wannan abu ya biyo bayan wani abu da ake kallo wai shi wayewar kai! Babu wani addini cikin duniyar nan da yake sako-sako da tarbiyyar al’umma a ko ina cikin duniya.
Tarbiyyar jama’a ita ce ke tafiyar da rayuwar al’umma gaba daya. Menene dalilin rashin tarbiyya a yanzu cikin al’ummah, khususan tamu a wannan lokaci? Da dai babu ko shakka siyasa ta cikin wata aba Dimokradiyya su ne asalin kawo cikas ga tarbiyya saboda karairayin da suka rataya bisa waccan kalma Dimokradiyya.
Gaskiya ne ita siyasa hanyar mulki kenan, wato kalma ce wacce take nufin mulkar jama’a. gaskiyar lamari ga duk mutumin da ya iski siyasar 1960 zuwa 1966, su wadancan ‘yan siyasar sun bi hanyoyi na taimaka wa jama’a bisa gaskiya da kyautatawa bisa yadda ya kamata, ba tare da nuna banbanci ba. Sannan sojoji sun yi mulki shekaru masu yawa wanda ‘yan Nijeriya sun koyi tarbiyyar sojoji wadanda suka banbanta da na ‘yan siyasa.
Shi soja bin umarni kawai ya sani, su kuma ‘yan siyasa wai bin ra’ayin jama’a kawai koda kuwa hanyoyin tarbiyyar sun sha banban da al’adu da kuma tsari mafi girma na addini.
Matukar mutum yana son kyakkyawar rayuwa to tarbiyyar addininsa ita tafi kyautatuwa gareshi. Duk da cewa tun shekarar 1999 muka dawo da mulki irin mulki na Dimokradiyya, amma ba mu ci burin wannan kalma ba tun da komai ya lalace ta fuskoki da dama, saboda jama’armu musamman samari ba sa girmama manya ba wai kawai masu mulki ba, kowa ba shi da kima wurin wadannan samari a wannan zamani! Ku duba dai yadda mutane kususan ‘yan Arewa suke kushe shugaba Buhari watakil saboda ‘yancin dan’Adam da siyasar Dimokradiyya ta kawo ta yau dan’Adam wanda ko da mara gaskiya ne, boye tasa cutar yake gami da ikon fadar wasu bankade-bankade.
Gaskiya duk mai mulki idan ababe marasa dadi suka faru tofa koda “natural” ne tofa shugaba shi yake da alhakinsu, yanzu na ga wasu mtane suna caccakar shugaba Buhari cewa domin me yake zuwa Daura kuma a kan me? Gaskiya fadin haka wauta ne daga wawa domin babu wani da na halal da za’a hana shi shiga gidan mahaifinsa matukar aibunsa bai shafi addini ba, yana kyau idan mutum zai yi batu to ya tsaya ya Ankara da ababen da zai ambata.
Gaskiya ne mulkin Shugaba Buhari ya sami kansa ciki kwanzama domin irin ra’ayin da gwamnatinsa ta runguma wadanda da yawansu suka takura wa ‘yan Nijeriya gaba daya!
Abubuwan a bayyane suke domin ‘yan Nijeriya musamman talakawa mun shiga halin ni ‘yasu, saboda tsananin talauci da ya addabemu, kuma wannan ya faru saboda matakai da gwamnati ta dauka tun lokacin Janar Babangida na shigo da wata hanya ta karya wuyan arzikin Nijeriya, wato wata muguwar hanayar karya tattalin arziki wai ita “SAP” wannan mashahuriyar keta ce wacce take lankwabe duk wata kasa da ta rungume ta tun wancan lokaci har lokacin da Janar Buhari ya hau mulki a shekarar 2015, sai ma abin ya yi kamari gwamnatin ta kara azamar bude hanyar rugurguza tattalin arzikin Nijeriya domin dadadawa Bankin Duniya da wata muguwar kafar Turai wai ita IMF.
Gaskiya domin kara wa gyambo gishiri sai rufe kan iyakokinmu, an ce wai domin hana shigowar makamai! Wannan rufe bodoji ya shafi ‘yan Arewa domin kayayyakin dake shigowa domin bukatar jama’a babu su, kodayake mun ce ‘yan Arewa, amma bodojin sun shafi ‘yan Kudu musamman garuruwan Yarabawa da kuma Cross Ribers tsakaninsu da kasar Kamaru koda yake sun yi iyaka da Benue ne ko Taraba, domin na ga Katsina Ala ko Benue ne ko Taraba! Gaskiya wadannan da wahalar rayuwa ta jawo wa gwamnatin Buhari bakin jini, duk da cewa har gobe jama’a basu san cewa akwai mutanen boye masu assasa wannan lamari domin gurgunta gwamnatin ba.
Ita gwamnatin Buhari ta gaji wasu abubuwa kamar Boko Haram, kama mutane domin a nemi kudin fansa, wannan ya faru tun sojoji a wurare kamar Delta da Kudancin Nijeriya ta Gabas, kowa ya san da haka – amma ababen sun fi kamari a Arewa wurin da Shugaba Buhari ya ce musu cima zaune sun fi yawa koda yake ga duk mai zirga-zirga cikin kasar nan zai fahimci cewa abin ya shafi kowanne gefe, dauki lokacin soja a Bendel ta yadda kowanne karamin yaro yana da bindiga musamman zamanin wani mugun dan fashi wai shi Anini!
Kaga ababuwan sun yi nisa tun tuni Nijeriya tana cikin matsanancin rikici tun wancan lokaci, sai dai yanzu inda idanuwa suka bude musamman a nan Arewa inda a da bamu san haka ba. Kamata ya yi mutane su gane cewa kamar yadda turawa kan ce “Seberal theatres of conflicts” wato “yawaita yaduwar masifu”.
Duk kasar da ta sami kanta cikin wadannan masifu sai addu’a ita ce kawai mafita tare da karfafa gwiyoyin sojoji da sauran jami’an tsaro amma ba kushe ba kuma duk wata gwamnati da tazo wadannan masifu ba za su kau cikin kiftawar ido ba, domin yaki ake yi da ‘yan gida Allah ya tsare.
Gaskiya tsarin Allah muke neman
Comrade Ibrahim Abdu Zango, shi ne shugaban Kano Unity Forum, ana iya samun sa a: 08175472298