Manchester City da Ilkay Gundogan sun cimma cikakkiyar yarjejeniya akan komawa kungiyar ta kasar Ingila domin ci gaba da taka leda.
Gundogan, mai shekaru 33, zai rattaba hannu kan kwantiragin shekara daya da City, tare da zabin karin watanni 12.
- Mutane 4 Sun Mutu, 6 Sun Bace Sakamakon Kifewar Kwale-kwale A Kano
- Mun Gano Hanyoyin Da Ake Satar Man Fetur A Nijeriya – NNPC
Dan wasan zai bar Barcelona a kyauta, shekara guda bayan ya koma kungiyar a watan Yunin 2023.
Gundogan ya koma Barcelona a bazarar da ta wuce, inda ya buga wasa 36 a kakar wasa ta farko, amma an gaya masa cewa, baya cikin jerin ‘yan wasan da sabon kocin kungiyar, Hansi Flick zai tafi da su bayan ya maye gurbin Xavi a farkon wannan bazarar.
City ta kasance kan gaba don tabbatar da dawowar Gundogan, inda dan wasan tsakiyar ya tattauna da Pep Guardiola kan yiwuwar komawa Manchester kuma kocin ya ba shi dama.
A baya Gundogan ya buga wasanni 188 a karon farko a City, inda ya lashe kofin Premier sau biyar, kofunan FA guda biyu da kuma gasar zakarun Turai sau daya.